Da alamaun za a Haramta hawan Mashin mai kafa biyu a manyan jahohin arewa kamar haka dan inganta tsaro.
Jahihin sun hada ne da Zamfara, Kano, Kaduna, Sokoto, Katsina, Naija, da Kebbi. Wayan nan jahohin na fama da matsalolin Masu garkuwa, Barayin Shanu, da rikincin makiyaya da manoma.
Yawan jahohin da aka haramata wa Hawan Mashina zai kara yawa kenan, wanda daman tin can an haramta hawan mashin a Birno, Yobe, da kuma Adamawa. Duk wayan nan jahohin suna areacin Nigeria ne, kuma su suka fi ko ina sake zabar wannan chanjin. Yayin da babu jaha ko daya da aka haramta hawan mashina a Yankin Kudu.
Talaka, a zalunci shi, bai san an zalunce shi ba sai talakan arewa.
Haramta hawan Mashin a wayan nan jahohin, zai sake haifar da wasu matsaloli ne wanda ciki akwai kunci rayuwa. Mafiyawan 'Yan Acaban nan magidanta ne masu iyali, kuma da wannan sana'ar suka dogara, suka kai zuciya niasa dan su nemi halalin su.
Masu karatu me raayin ku?
Tare da wakilin Shafin Ma'asumah --Idishia Jos.
Tags:
Labaran Duniya