Kuyi shere Domin Wasu su amfanana
Ma'asumah Nigerian News Updates
Ga wani bangare na jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)ya yi a ranar Alhamis 10/9/2009 dangane da shirin da gwamnatin Umaru Musa Yar’adua ta yi na kashe shi da ganin bayansa a kwanakin qarshe na watan Ramadana:
“….To, sai muka samu wani abin da ake ce ma ‘Blue Print’, rubutaccen bayani kan tsarin da aka yi, (a cikinsa) sai aka ce, tsakanin 16 zuwa 19 ga watan Satumba za a yi ‘Operation’. Sai aka fadi a ‘Blue Print’ na ‘Operation’ din, cewa za a yi a Zariya ne. Kuma ni ban taba ganin wannan kalma ba, amma wannan na ganta an rubuta a ‘Blue Print’ din gwamnati; (cewa) za a yi abin da suka kira ‘Massacre!’. Kun san ‘Massacre?’
Kisan-kiyashi! Za a sheqar da jinane! Wato, suka ce za a kashe kowa ne, da mai zanga-zanga (Muzahara) da dan kallo da mutumin gari. Kuma har suka ce za a tsaya a ‘Check-point’, don wai sun yi kuskure a Maiduguri, sun riqa harbe mutane a ‘Check-point’ ido na gani, saboda haka wannan karon ba za su yi wannan ba.
Za su tsaya a ‘Check-point’ ne sai su kwashe mutanen da suke son kashewa su kai su wani wuri sai su yi abin da za su yi.
Sannan kuma (suka ce) duk garuruwan da ke kusa da Zariya, za su bude masu wuta, cewa ainihin Shi’a sun gudu sun je garin, wanda ya ke nufin za su bude wuta ta kowane hali kawai akan mutane!Cikin daren jiya, (9/9/2009) sai muka samu labarin cewa, barikin soja an shirya su a kan batun za a yi wani ‘Operation’ a jiyan. To dama akwai wata magana da na ji, cewa su sojoji an musu jawabi an fada masu cewa a goman qarshen watan Ramadan ‘yan Shi’a sun ce wai za a yi juyin-mulki.
To kuma za a yi qoqari a hambare wannan juyin-mulkin. To ka ga suna shirya qwaqwalen soja da cewa za a aika su su yi kisan kai kenan.
To, sai jiya cikin dare labari ya zo mana cewa, lallai an tara soja an fada musu cewa a cikin daren za a yi ‘Operation’.
Aka ce musu ‘Operation’ din kamu ne, amma idan kamun bai yiwu ba, za a yi mataki na gaba.
Amma su masu fada mana labarin sun ce ba su san wa za a kama ba, ba su san kuma meye mataki na gaba din ba.
Ala-ayyi-halin dai, muna nan muna sa ido. Sai labari can cikin dare ya zo mana daga Abuja, (wannan kuma amintaccen ‘Source’ ne), cewa ‘Operation’ din nan a gidan da nake kwana za a yi, kuma abin da suka yi niyyar yi shi ne za su yi ‘Bombing’ din gidan ne. Bombing sosai! Za su jefa bam su tarwatsa gidan gaba daya!
(Yadda za a yi ‘Operation’ din shi ne); Za a aiko da ‘Signal’ ne daga Abuja, in an aiko da ‘Signal’ cewa a yi ‘Carryout Operation’ din, akwai wadansu (jami’an tsaro) da za su taso daga Kaduna, sai su iso su hadu da na Zariya, sai a wucewannan aikin na tarwatsa gidana da bom! To, dama har akwai masu ce min, to ko daidai wannann lokacin zai zama ba na gidan ne? Na ce Allah ya sauwaqe!!
KARANTA WANNAN:- Sojoji ne Suka fara bude kofar kashe-kashe a fadin kasar nan
Gidan da ake so a tarwatsa, ina amfanin na rayu bayan an tarwatsa iyalina?!
To, amma muna da labarin cewa sun ce za su gama da al’amarin Zakzaky ne gobe! Zuwa gobe Juma’a su gama.
Mai yuwuwa tunda ba su yi jiya ba, ko yau da daddare za su zo.Har ma, muna da labari a nan unguwar da na ke zaune da ake ce ma Gyallesu, akwai wasu mutane daidaiku, duk cikansu ‘yan qungiya (Wahabiyawa) ne, lallai sun bar unguwar. Kuma an ji ta bakinsu cewa, za a yi kisan kiyashi ne, saboda haka ko kusa da unguwar kar wani ya je, tunda za a yi kisa, saboda haka sai bayan an gama kisan za su dawo.
Ku masu yunqurin kisa, in dai kisa ne an kashe mutane wadanda suka fi ni. Saboda haka ba abin mamaki ba ne a kashe ni. Amma ina ganin babu buqatar ku saka Bom ku tarwatsa gidan da nake kwana. Domin a gidan nan akwai mahaifiyata ‘yar shekaru 88, kuma ba ta muku (laifin) komai ba. Akwai kuma yara qanana, wadanda su ma ba su muku (laifin) komai ba. Ni kasha ni ba wani abu ba ne, kuna iya kashewa, an kashe wanda su ka fi ni a wannan zamanin da da, saboda haka in ma an kashe ni Sunnah ne. Amma mene ne naku na qiyayya da za ku yi wannan?
Musamman kai Umaru Musa Yar’adua, wanda suka sa ka, suka ce wai kai ne shugaban qasar nan, kuma ka ke tunanin cewa za ka burge su. Yanzu za ka burge Amurka da Isra’ila idan ka kashe Al-Zakzaky. Sun dora ka a kan cewa yanzu za ka yi kisan kai, kila don ka samu fuska a wajensu. To, Sunnah za ta maimaita kanta. Ni, na yi burin a ce wanda zai kashe ni, ya zama wani mutum wanda ba shi da rabon Lahira ne, amma ni ka
ban mamaki, saboda ina jin tausayinka, kamar yadda nake jin tausayin yayanka da aka kashe. To, amma in haka ka so, shikenan, Falillahil-hamd! Amma dai roqona shi ne ka kashe ni ni kadai, ba buqatar ka yi ‘Massacre!’, ba buqatar yin kisankiyashi. Ba buqatar kashe mahaifiya da ‘ya’yana, sukai maka mene? Da kuma makwafta ma, duk sukai muku mene?
Ku kuma wadanda za ku yi kisa, kar ku dauka za ku samu wani matsayi ne. Ita da’awa ba za ta mutu ba.
Don an kashe ni ba yana nufin shi kenan da’awa ta mutu ba. Insha Allahu sai dai ta yi qarfi, domin ainihin da’awa Alhamdulillahi, ta riga ta shiga zukatan mutane, kuma lallai bindiga ba zai bindigeta ba! Ko da kuwa kun yi abin da kuke cewa za ku yi wai shi kisan-kiyashi,‘Massacre’!
Ga wadanda ake kira Malamai; Hukumar da take cewa ba ruwanta da addini, ko dutse kana iya bauta ma, ko itace. Furuci suke yi sosai muraratan, ko dutse ko itace kana iya bauta ma, to sune kuma za su kashe muku wadansu ma’abota addinin da ba ku so, sai su barku ku ku yi addini?! Ma’ana su za su muku jihadi addininku ya tabbata?! Haka kuke tsammani? Sai mu ce muku, to wannan abin da ku ke tunani mafarki ne. Ba zai yiwu ya zamana wai nizamin da ba rowan shi da Allah, ba rowan shi da addini shi ne zai tabbatar muku da addini, ya maishe ku Malamai ba!
Al’ummar Musulmi kuma don su gane, (su al’umma suna iya ganewa); In ka ji wani mutum yana da’awa, yana cewa a kashe Musulmi, sawa’un Musulmin nan ko mene ne ra’ayinsa, ko ya ce masa dan tatsine ne, ko ya ce masa dan qala-qato, ko ya ce masa dan Boko Haram, ko ya ce masa dan dariqa, ko ya
ce masa dan Shi’a, ko ya ce masa dan mene ne, in dai ya ce a kashe Musulmi ne mai shaidawa da La’ilaha illalah, Muhammadur Rasulullah, to wallahi summa tallahi, Yahudawa yake ma aiki! Kuma maqiyinka ne kai, in ka yi Imani da La’ilaha illalah, Muhammadur Rasulallah, ko meye ra’ayinka!
Mutum ko meye ra’ayinsa a addini aqalla dai Musulmi ne, to yaushe kai za ka nemo wanda ba ruwansa da addini, bai san addini ba, shi ne zai maka jihadi addininka ya kafu? Ballantana in dai Musulunci ne ka ke yi da gaske, to ya kamata ka ji tausayin wanda ka ke ganin bai gane gaskiya ba ne, in kai kana kan gaskiyar ne. Ka kira shi da tausayi domin ya gane, don shine sunnar na farko.
Amma ba zan qarkare maganar nan ba sai na yi muku albishir, cewa ko an qi ko an so addinin Allah zai tabbata! Ba yadda za a ce bakin bindiga ko Bom ya tarwatsa da’awa ya zuwa ga Allah! Saboda da’awar nan ba ta doru a kan a kashe
wani ba, ko ana barazana ga rayuwar wani ba, ta doru akan hankali ne da ilimi da kuma hujja, shi ne kuma mutane suke ji su gamsu.
Ni dai kam Alhamdulillahi, gaskiyar magana ita ce, ni abin alfahari ne ya zama an kashe ni a kan abin da nake yi. Abin alfahari na ne. Dama ko ba a kashe ni ba, yau shekaru 30 kana ta da’awa, abu daya, kuma ana ta yunqurin a kashe ka sam baka kasu ba, kuma har da’awa ta kafu daram, ba yadda za a yi da
ita. Komai tsiyan mutum dole sai da’awar nan ta habaka ta tabbata. Kuma ba mu tsammanin za ta tabbata muna nan ne, amma dai za dai ta tabbata din! Saboda haka idan wannan (yunqurin kashe ni) ne ya zama ya muku, sai mu ce to, shi kenan. Kar ku dauka mu za mu yi ko gezau! In ma yau da daddare ne ku ke so ku zo, ko ma wani dare ne, to ina nan a gida.
Amma dai kamar yadda nake roqonku, in kun ji roqon shi ne, ba buqatar ku kashe mahaifiyata da ‘ya’yana da iyalina. Ni kawai ku zo (gareni) shikenan, duk yadda kuke buqata sai ku yi abin da za ku yi.Insha Allah.”
_______________________________
Ma'asuma Nigerian News Update,
[Daga Littafin Yunkurin kashe shaikh Zakzaky acikin shekaru goma 10].
_Visit Us@
www.maasumablogspot.com
Wakilinmu,
®__Mahadi Tukur Almizan_
™help Us share
Tags:
Jawaban Sheikh Zakzaky