YAKI YA TARDA SHUGABAN KASA BUHARI HAR GIDA GARIN DAURA

YAKI YA TARDA SHUGABAN KASA  BUHARI HAR GIDA GARIN DAURA.

✍️
MSN 012.
MAGAJIN GARIN DAURA. 


Dazu ne bayan sallar magariba labari ya riske mu cewa wasu yan bindiga da ba'asan ko suwaye ba suka kai hari garin Daura, kofar gidan magajin garin Daura, kuma har sunyi nasarar tafiya da magajin GARIN DAURA ALAHJI MUSA UMAR, WANDA TSOHON JAMI'IN HANA FASA KWAFRI NE (COSTUM).

Magajin garin Daura ya kasance siriki ne ga shugaban kasa, Don haka wannan ba karamin abin kaico bane tare dayin Allah wadai! Haka kuma wannan ya nuna yadda ake yunkurin son ganin an tozarta shugaban kasa.

A bisa wannan dalili nake ganin yazama wajibi ga shugaban kasa yasake duba yanayin shugabancin tsaro Domin wannan Abu yayi mummunar baci, madamar za'azo har garin shugaban kasa ayi irin wannan ta'adin to ina ne kuma mutane zasuje suyi tunanin sun tsira?

Gaskiyar magana wallahi akwai matukar abin tsoro a wannan lamari Domin mutumin da yake babba bai tsira ba to ina ga mu talakkawa yan kwashi kwaraf yaya zamuyi da kanmu?

Daga karshe muna Mai Kara jaddadawa akan lalle akwai bukatar sake Duba yanayin tsaron kasar nan Domin abubuwa suna Kara dagulewa.

Da FATAN ALLAH YAKAWO MANA KARSHEN WANNAN MASIFA YA KUBUTAR DA MAGAJIN GARI TARE DA SAURAN MUTANEN KASAR NAN DA AKAYI GARKUWA DASU, MU KUMA ALLAH YA TSARE MU DA TSAREWARSA.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post