-A'isha M Khazimiyyah.
Alhamdullahi kamar Jiya ne muke cikin watan Rajab! gashi har Sha'aban ya wuce, yau gamu cikin Ramadan, Iko sai Allah. A cikin qidatar watannin Muslumci Watan Ramadan Wata ne na 9 cikin watan ni 12 na Musulumci, kuma wata ne da yafi su. Kamar yadda kowa ya sani Watan Ramadan ba irin kowa ne wata ba ne, domin wata ne da ake rubanta aiyukan bayi. Kuma kamar yadda aka saba duk Watan da yazo Malummanmu na mana bayani a kan falalar wannan watan, munasabobi na watan da ayyukan ciki.
Haka shi ma Watan "Ramadan" ya ke da nasa falalar. Ramadan ya tara nasa falaloli masu tarin yawa, idan Mutane suka bincika dan gane da watan za su gani, kamar yadda Manzon Rahma (S) a ka samu hadisai da dama a gunsa dan gane da watan.
A duk cikin Watanni 12 na Musulumci babu wani wata da yake da falaloli da darajoji masu yawa kamar watan "Ramadan". Wata ne wanda Allah (T) a cikin sa ya ke 'Yanta Bayinsa daga wuta, wata ne wanda Allah (T) ke nunnunka Ayyukan Bayinsa a ciki, wata ne wanda a cikin sa tun daga farkonsa har qarshensa qofofin wuta a kulle su ke, qofofin aljanna kuma a bude suke, wata ne wanda a cikin sa ake daure shaidanu, wata ne wanda a cikin sa Allah (T) ke gafarwa bayinsa zunubinsu baki daya. Wata ne wanda a cikin sa Allah (T) ke daukaka Darajojin Bayinsa, wata ne wanda Allah (T) a cikin sa yake tsarkake Bayinsa Ya kuma kusantar dasu gare sa.
A'Isha Muhammad Kazeemiyya Potiskum |
Watan "Ramadan" shine watan da yayi dace a cikin sa Allah ya sanya wani dare wato daran "Lailatul-Qadr" wanda ibada a cikin daren tafi ibadar wata Dubu. Wata ne na samun tawaya fiye da sauran watanni, yana da matsayin na shugabannin watanni. A takaice dai watan Ramadana Ba shi da tamka. Dan a cikin sa ne alkairi da albarkatu ke sauqa.
Allah Ya sanya mu a cikin wanda Allah (T), zai 'yantar. Ya bamu albarkacinsa da Falalolinsa. Allah Ya sanya duk aikin da zamuyi a wannan watan ya zama karbabbe ne a gurun Ubangijinmu. Yanci da tsawan rayuwa, albarka, hasken fuska wadatar zuci, ya nun ka a Wanda ya kasance mai yiwa salati a Monzon Rahama Da iyalansa. Allah ya tausaya mana ya jibanci lamarinmu a kan Jagoranmu.
Tags:
Yanar gizo