WAFATIN SAYYADAH KHADIJAH (S.A) !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A irin wannan rana ce 10 ga Ramadan, shekara ta 10 bayan aiko Annabi (S A.W W) a matsayin dan saqo, kuma shekara 3 kafin Hijrarsa (S.A W W) Allah ya karbi ran wannan baiwar Allah wacce muslimci ba zai taba mantawa da ita.
Sayyadah (S A) ta kasance babban bango abin jingina ga Manzon Allah (S A W.W), domin tana cikin mafi girman wadanda suka ba shi (S.A.W.W) da kuma taimakonsa don isar da saqon Allah (T).
Muslimci bai ruwaito dukiyar da ta amfanar da muslimci da kuma taimakon al'umma kamar tata ba, wannan dalili yasa Annabi (S A W.W) ke cewa;
" BA DON KARIYAR ABU 'DALIB DA DUKIYAR KHADIJAH DA KUMA TAKOBIN ALI BA, TO, DA ADDINI BAI TSAYU DA QAFAFUNSA BA ."
Sayyadah Khadijah (S.A) ita matar Annabi ta farko, kuma wacce ya fi yin fahari da ita, domin tsahon zamantakewarsu ba ta taba bata masa rai ba, wasunta kuma har ayoyi ne suka sauko a kansu don cutar da Annabi da suka riqa yi da harsunansu.
Saboda kyautatawarta gare shi, bai taba hadata da wata (kishiya) ba tsahon zamansu. Amma bayan wafatinta sai da ya auri mata masu yawa ko zai sami irin wacce ya rasa, amma Allah bai yi nufin haka ba.
Ita ce matar da ta sami busharar Aljannah tun daga duniya daga cikin matansa. Ganin wannan karramawar da Allah ya yi mata daga duniya yasa Annabi (S.A.W.W) ya riqa ambaton sunanta da yabonta bayan wafatinta (S.A), har wata daga cikin matansa ke tsarginsa kan haka.
Wannan musifa ce da ta sami Annabi da dukkan wani me imani. Manzon Allah (S.A.W.W) ya ambaci wannan rana da ranar musifa.
AMINCI YA TABBATA A GARE KI RANAR DA AKA HAIFE KI DA RANAR DA KIKA MUTU, DA KUMA RANAR DA ZA A TASHE KI KINA ME RAI.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.