TAMBAYA DA AMSA A WATAN RAMADAN


TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, wasannin tashe da ake yi idan azumi ya kai kwana goma, menene asalinsa, kuma ya matsayinsa a Musulunci?
SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY


SHAIKH ZAKZAKY: 
Al’ada ce dai kawai. Kuma abin mamaki kusan ko’ina a kasashen musulmi suna wannan al’ada din, yakan bambanta tsakanin wannan wuri da wannan wuri, kasashen Larabawa suna yi, wasu wurare ya zama zaunennan abu, mai yiwuwa saboda yanayin rayuwa irin ta da mutanen da, da duhu, da kuma sai an ta da mutane. Amma kuma yanzu ya zama kawai wasannin ne, ba a bukatar sa. Amma a da ana bukatar sa sosai don a tashi mutane su dafa abinci, amma yanzu ba a bukata, saboda mutane suna da agogwanni masu karaurawa, da kuma yanzu ma daren ma ba a cika barci sosai ba. Amma dai al’adar mutane ne, kuma ba laifi da shi, tun da ba an ce aibada ne da aka ruwaito ana yi ba. Al’ada ce kuma ba ta yi karo da shari’a ba, saboda haka ba komai. Allahumma sai dai in akwai wasu abubuwa da ake yi a tashen, wanda ya saba ma shari’a, sai a ce to su a bar su. Amma shi tashe a kashin kansa kawai al’adar mutane ne.
✍️
ISHAQ SAGIR MAGAJI

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post