TA BABBE NE WANDA WATAN AZUMI YA WUCE ALLAH BAI GAFARTA MASA ZUNUBINSA BA.

              Inji -Sheikh Adamu Tsoho Jos.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates. Tare da -Idishia Jos.

Manzon Allah (S) yana cewa; Duk wanda yayi sadaka a  wata na Ramadan sakamakonsa shine Allah zai gafarta mashi, duk wanda ya kyautata ma wanda suke karkashinsa, Bayi ne Hadimansa ne, Matarsa ne, Yaransa a shago ne ko a wajen sana'a sai ka kyautata musu sakamakon ka a wurin Allah shine Allah zai gafarta maka, ko mace ne idan ta kyautata ma Mijin ta ko kuma Yaranta. Wanda ya kyautata dabi'unsa a cikin watan Ramadan Allah zai gafarta masa. Wanda ya hadiye fushinsa an cuta ma kayi juriya ka hadiye fushi to Allah (T) zai gafarta ma, wanda ya sadar da zumuncinsa a cikin watan Ramadan ko a Iyaye ko Abokai ko Makocin ka lallai Allah zai gafarta maka.

Wannan wata na Ramadan bai zamo kamar sauran watanni bane, lallai wannan wata na Ramadan in ya fuskanto to yana fuskantowa ne da albarka da Rahma, haka kuma idan watan Ramadan ya kare to yakan juya baya ne da gafarar zunubi, yakan tafi da zunuban mutane wannan wata ne wanda yake kyawawan ayyuka akan ninninka lada a cikinsu, duk wani aikin alkhairi da mutum yayi a wannan wata to karbe be ne a wurin Allah (T). Manzon Allah yana cewa ; wanda yayi Sallah a cikin wannan wata na Ramadan yayi Sallah wa Allah raka'a Biyu na Nafiloli to Allah (T) zai gafarta mishi.

Kada dukkan wannan wayyuka ne da aka kwadaita mana, a watan Ramadan ana kara yawaita ayyuka ne domin karin samun lada, Imam Ridha (As) yana cewa; Lallai marar arziki tababbe shine wanda wannan wata ya fita ba'a gafarta masa zunubansa ba, to shi a wannan lokaci ya tabe yayi asara. A lokacin da masu kyautatawa zasu rabauta da sakamako na Ubangiji mai karamci. Watan Ramadan sai fa marar rabo shine baya rabauta a cikinsa, wanda yake darenshi da ranar shi gabaki daya ba abinda yake sai alkhairi sai albarka sai na rahma, duk wani motsi idan kayi lada ake rubutama a cikin watan Ramadan.

Yazo a ruwayan hadisi daga Imam Ridha (As) yana cewa; Manzon Allah ya mana huduba a watan rana yake cewa lallai fa ku sani watan Allah mai albarka mai rahama wanda ke cike da gafara ya fuskanto ku, wannan wata ne wanda yake a wurin Allah mafificin wata yana da girma yana da daraja kwanakinsa kuna sune mafificin kwanaki darerakunsa kuma sune mafificin dareraku, kuma sa'oi dake cikin wannan wata ko dare-raku ko yini to sune mafificin sa'oi ko wanne awa daga cikin awowi 24 na kwanne rana to shine mafifici. Lallai wannan watane wanda aka kiraku izuwa liyafa na Allah wato watan Ramadan wata ne na zuwa liyafa, wa ya kira wannan liyafan shine Allah Azza-wajalla.

Hoton Sheikh Zakzaky (H) wanda aka daga jiya a babban Masallacin Juma'a na  Jos a lokacin Muzaharar #FreeZakzaky.

Saboda haka watan gabaki daya yakan zamo faida ilahiyya, wanda tun daga 1 ga wata har 30 ga wata ( 24hour ) kowanne rana yana cike da Rahmane yana cike da alkhairi yana cike da rahma yana cike da albarka ne sabida haka watan gaba daya ladane a ciki. Shiyasa aka mana baiwa da watan Rajab da watan sha'aban shi musulmi ake so mutum ya wanke daudanshi a cikin watan Rajab ka tsarkake ganganjikin ka. Shi ko watan Sha'aban kayi amfani dashi wajen yin kwalliya na ganin watan Ramadan. Kuma an sanya ku a wannan wata wanda aka sanya ku ga liyafa na Allah (T) wanda Allah ya karramasu. Shi yasa ba'ason mai azumi ya yawaita wanke bakinsa bayan Sallah la'asar sabida warin bakin mutum Allah yafi son shi.

Manzon Allah (S) yana cewa numfashin ku a cikin wannan wata tasbihi ne. Za'a rubuta maka lada Subhanallahi duk numfashi da zakayi za'a rubuta maka lada subhamallahi, kunga yazo a hadisi subhanallah tumla'ul mizan. Yanzu da nacev subhanallah an ban lada wanda ya cika mizani, koda a watan Azumi bakace subhanallah ba to numfashin ka da zakayi ana rubutama ladan tasbihi ne. Sannan bacci da zakayi a wannan wata za'a rubuta maka ladan ibada ne to kaga me ka rasa ? Numfashin ka tasbihi ne haka bacci ibada kuma aikin ka karbebe ne duk aikin da kayi lada ne, sannan duk addu'an da kayi karbebiyace domin Allah yana jin kunyan bawa ya mayar da hannunsa ba tare da Allah ya biyawa bawa abinda ya roka ba.

A watan Ramadan karbuwan yafi akan sauran watanni, don haka addu'a da zamuyi to addu'a karbabbiya ce a cikin watan. Don haka ake son mutum ya yawaita addu'a ya yawaita aikin alkhairi a wannan wata. Kayi addu'a da niyya tsarkakakkiya ya kuma datar da kai da yin azumi na hakika ta banyan kiyaye ka'idodi da sharadi na ita Azumi kuma ya datar da kai ga karatun Qur'ani. Manzon Allah (S) yana cewa; lallai tabebe marar arziki shine wanda aka haramta masa gafarar Allah a cikin wannan wata mai Girma, duk wanda wannan wata Ramadan ya wuce bai samu gafarar Allah ba to wannan ya zamo tabebe bashida rabo.


#FreeZakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post