-Sheikh Adamu Tsoho Jos jiya a lokacin da yake gabatar da Tafsir a Garin Jos.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates
Tare da Wakilinsu -Idishia Jos.
Suratul Hujurat itace sura ta Arba'in da Tara (49) a cikin jerin surori na Alkur'ani tana da Ayoyinta (18) kuma surface wanda aka saukar a Madina illa Aya daya kamar yadda Malaman tafsiri sukayi bayani. Tana da kalmomi Dari Uku da Arba'in da Uku, ita surane da ta kunshi bayanai ne na ladibobi da Allah (T) ya ladabtar da muminai dangane da yadda zasuyi mu'amala tsakanin su da Ubangiji da kuma tsakanin su da ma'aikin Allah Muhammad (S). Wannan yana nuna mana cewa shi musulunci addini ne da ya ginu akan tarbiya akan Aqlak ( dabi'u ), dan haka ita sura din ta kasance tana koyar da yadda zamu dabi'antu da kyawawan dabi'u wajen mu'amalan mu da Ubangiji da mu'amala mu da Manzon Allah (S), a lokacin guda kuma da mu'amalan mu da junan mu.
Wannan sura tana da falala kamar yadda aka Rawaito a ruwayan Hadisai na Manzon Allah (S), yazo a cikin kawasul Qur'an, An rawaito hadisi daga Annabi (S) yana cewa; Wanda ya karanta a nan sura Suratul Hujurat, za'a bashi lada adadin wanda suka yuwa Allah (T) da'a, da kuma adadin wanda suke sun sabawa Allah (T) lada sau goma. Wato adadin duk masu da'awa Allah (T) tun daga farkon duniya har karshen ta, haka kuma adadin wanda suka sabawa Allah (T) za'a nin nin ka mai lada sau goma. Wanda kuma ga rubuta wannan ya rataya shi to a cikin yaki ko husuma Allah (T) zai cire mai tsoro, inda wani abu da kake tsoro to indai kana tare da ita Allah zai amintar da kai, kuma Allah zai bude kofofin dukkan alkhairi.
A cikin Kitabul sawabul A'amal yake cewa; Duk wanda ya karanta ita wannan Sura na Hujurat a cikin kowanne dare ko kowanne yini tamkar zai kasance tamkar yana ziyartan Manzon Allah (S) ne. A cikin Majma'ul Bayan Hadisi daga Ubait Bin Ka'ab yana cewa; Wanda ya karanta ita wannan Sura Suratul Hujurat za'a bashi ladan kyawawan Ayyuka Goma (10). Sadiq yana cewa; wanda ya rubuta wannan Sura din ya rataya a jikin wanda shaidanu suke binsa to Allah zai amintar dashi daga shedanunda suke binsa, kuma ba zai komo gareshi ba, Allah zai amintar dashi ga dukkan abinda yake tsoro. Ita kuma Mace idan tasha ruwan wannan, to Nonon ta zai bubbugo kamar Macen da battada Ruwan Nono kenan idan ta haihu aka rubuta mata wannan Sura din Allah zai bubbugo da Nonon ta, kuma za'a kiyaye dan ta kuma za'a amintar da ita daga dukkan wani abun tsoro daga Allah (T).
Wasu daga cikin masu sauraron Tafsir jiya a Jos lokacin da Sheikh Adamu Tsoho Jos yake gabatarwa a Unguwan Rogo Jos. |
To a Kullum mukan yi bayani falala na Sura da ake kawo wa ba yana nufin kawai mujarradin ainihin lallaka na harshe bane ki baki, a'a ana nufin aiki ne da ita Sura din ya zamo Suran ka siffantu da Umarnin da ke ciki ka hanu da hanin da ke ciki. To idan kayi wannan ya zamo an ganka anga Suratul Hujurat a aikace. To shine zaka samu falala da daraja da aka kawo cikin wannan ruwayoyin. Tare da cewa surace takaitacciya amma ta kunshi abubuwa mai yawan gaske masu girma, ta kunshi Hakakik na ka tarbiya wanda Allah ya tarbiyantar da dan Adam kuma asasi na ainihin al'umma musulma al'umma ta gari. Har shashin masu tafsiri sun ambaci wannan sura da Sura ta dabi'u saboda abinda take koyarwa. Ita wannan sura mutum ba zai samu falalan taba har sai ya siffantu da aklak dake ciki.
Ita wannan sura ta fara be da tarbiya ko ladaftarwa wanda Allah (T) ya ladabtar da muminai abisa tarbiya ko ladabtarwa mafi daukaka dangane da abinda ya shafi shari'an Allah da kuma umarni na Manzon Allah (S). Shine cewa kada muminai su kulla wani al'amari koko su bayyanar da wani ra'ayi koko su yanke wani hukunci a gaban Manzon Allah (S), har sai sun nemi shawaran Manzon Allah (S) kuma suyi riko da irshadin da Manzon Allah ya bayar wanda yake cike da hikima. Shine Allah ya fara sura din da; Bashi halarta India muminine ya zamo ya gabatar da wani al'amari ko ya yanke wani hukunci ko ya zartar da wani Abu a gaban Manzon Allah (S) ba tare da ya umarci Manzon Allah (S) ba, kokuma in Allah da Manzo suka yi hukunci to baka da ikon da kai wuce gaba da Manzon Allah (S) , ko kace kai ga naka.
Sannan ita wannan Sura ta ciru zuwa ga wani ladabi ko tarbiya na daban shine, mutum ya rage muryansa a lokacin in yana magana da Manzon Allah (S), sabida girmama matsayin Manzon Allah (S) matsayinsa mai daraja, da kuma girmama matsayinsa madaukaki domin shi Manzon Allah ba kamar sauran mutane bane, shi ma'aikin Allah ne shine shugaban halitta ya zama wajibi kowa da kowa ya bishi kuma ya saurara mishi. Yana daga cikin wajibin muminai ya zama sun ladabtu sun nuna kyakkyawan ladabi da tarbiya a wajen maganan su da Manzon Allah (S) tare da ainihin girmamawa da jinjinawa da kuma wato girmama sha'anin Manzon Allah (S), don haka idan kana gaban Manzon Allah ba zaka yi magana ka daukaka muryan kaba.
Wannan wani bangare ne na karatun Tafsirin Alkur'ani Mai Girma da Sheikh Adamu Tsoho Jos ya gabatar jiya da dare a Zaman karatu na rana ta Biyu a muhallin Hussainiyatu Zakzaky (H) dake Unguwan Rogo Jos.
#FreeZakzaky
Tags:
Munasabobi