SINADARIN ABINCI MAIGINA JIKI DAMGIN BITAMIN

Gidan ki naki ne yar uwa!!

Daga (M.N.N.UPDATES)
.Sinadarin abinci mai gina jiki dangin Bitamin yana taka babbar rawa wajen ingancin abinci mai gina jiki wanda ake samu a wasu nau'o'in abincin da muke ci yau da kullum, kuma wannan sinadari kasantuwarsa a cikin jiki yana zama dole saboda tarin ayyukansa,domin samun ingancin rayuwar halittar jiki.

Rabe-Raben Sinadaran Bitamin

Masana kimiyar abinci sun kasa sinadarin Bitamin gida biyu,kamar haka :
1.Wadanda ake fitarwa daga kitse ko maiko.
2.Wadanda ake samu daga abinci mai ruwa-ruwa.
Rukunin Abinci Masu Gina Jiki Wadanda Ake Fitarwa Gaga Kitse:Bitamin A, Bitamin D, Bitamin E, Bitamin K.

    Bitamin A
Ana samun irin wannan nau'in sinadarin abinci mai gina jiki a cikin wasu nau'o'in abinci kamar kwai,kifi,man kifi,madara,man shanu,man ja,man burodi da sauransu. Kodayake jiki ya na iya samawa kansa irin wannan sinadarin na Bitamin A.idan aka ci wasu kayan rafi kamar karas, kankana manja da sauransu.
Amfanin Sinadarin Bitamin A Ga Jiki
Kasantuwar wannan sinadari a cikin jiki ya na hana kwayoyin cuta sakewa a cikin jiki ta hanyar takura rayuwarsu da duk abinda zai taimakawa jin dadin rayuwarsu a nan. Sannan samun irin wannan sinadari ya zama dole ga ingancin halittar ido,da dukkan amfanin da idon mutum ke yi. Misali,gani cikin duhun dare sai da taimakon wannan sinadari. Idan kuma aka rasa wannan sinadari a cikin jini ya na iya haifar da ciwon dundumi ga Mara lafiya watau ciwon rashin gani cikin duhun dare.
      Bitamin D
Ana samun irin wannan sinadarin gina Jiki dangin Bitamin D. A cikin wasu nau'o'in abinci kamar kifi, hanta,kitse,kwai,madara,manja da sauransu. Kuma mutane da dabbobi sukan sami irin wannan sinadari daga hasken rana wanda kan ratsa fatar jikisu ya kuma bai wa jikin wannan sinadari.
Amfanin Sinadarin Bitamin D. Ga Jiki.
Yana inganta wasu sinadarai wadanda ke da matukar amfani ga halittar kashi a jiki da kuma ingancin sa. Rashin wannan Sinadari a jiki yana yin sanadin wata cuta mai lalata kashin mutum,musamman yara kanana,watau ciwon gwame.
      Bitamin E
Irin wannan nau'in sinadarin gina jiki watau dangin Bitamin E,ana samun sa ne daga wasu nau'o'in abinci kamar ganyen latas,salad,kwai,masara,gero,madara,gyada da sauransu. A wasu dabbobin an samu tabbacin cewa, rashin wannan sinadarin gina jiki dangin Bitamin E. Lalle yana hana haihuwa,koda yake bincike bai tabbatar da hakan a jikin dan Adam ba.
Amfanin Sinadarin Bitamin E.
➡ Yana karawa tsokokin jiki inganci da lafiya.
       Bitamin K
Daga nau'o'in abinci irin su kifi ganyen itatuwa,hanta,kayan rafi iri-iri,ake samun irin wannan nau'in abinci mai gina jiki.
Amfanin Sinadarin Bitamin K. Ga Jiki
➡Dole ne Sinadaran gina jiki dangin Bitamin K.su kasance cikin jiki domin taimakawa yayin da ake bukatar kamewar jini a wani Sashen jiki.
➡Cututtuka da dama za su iya kama kama Mara lafiya sakamakon karancin wannan sinadari a jinin mara lafiya. Daga cikin irin wadannan cututtuka akwai wata cuta wadda jini zai rika zuba ko kwarara daga jikin Mara lafiya musamman ta sashen cibiya da sauransu wurare,kamar wurin da aka ji rauni,amma sai jinin da ke zuba ya ki tsayawa,watau ya yi ta kwarara.

*Wakilin Ma'asumah 🇳🇬Nigeria🇳🇬 News Updates.*

*@Auwal M. Tukur*

  29/5/2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post