SHIN KO KUNSAN MENE CIWON SANYI NA (INFECTION).

FILIN CUTA DA MAGANI



Shin ko kun san wace irin illa yake yiwa al uma kuwa?

           

Daga : Ma'asumah Nigerian News Updates (M.N.N U)

Tareda: Jibril Usman Sarki 


Da farko menene infection sabida in har baka san cuta ba to maganar ma bada maganinta be taso ba. 

Infection: ciwon sanyi wanda ake kira toilet infection. wannan suna yensa ne gama gari. amman a kimiyance muna cewa sexual transmitted disease (STDs).

Wannan ciwo na infection ciwo ne da kwayoyin cuta na Bacteria da fungal ke haddasa wa. wanda duka maza suna samunsa mata ma na samunsa. masu aure ko marasa aure kai harma jarirai in ba ai hankali ba wajen yanke cibi se uwa ta gogawa yaronta.

Hanyoyin kamuwa da wannan ciwon sun ban banta daga wani zuwa wani. Amman hanya mafi sauki shine ta saduwa (sex) shiyasa ma aurata da masu yawan Banza suka fi samun ciwon. Akwai masu lesbian da masu saka yatsa a farjin su se masu yin fitsari barkatai suma sukan dauka inda me cutar yai fitsarin. Masu cushe cushe na magun guna barkatai irin na matsi da niima suma sukan samu wannan ciwon. Se yawan saka pant me lema shima yana kawo ta. 

Alamomin wannan ciwo sukan ban ban ta daga wani zuwa wani, sannan zaka iya samun wasu daga alamun wasu kuma ba zaka samu ba. ya dan ganta da ciwon da kuma nau,insa. sannan ko kasha magani ko baka sha ba a farkon kamuwa da cutar alamomin xasu 6ata a zahiri kaga kamar ka warke amman a batini sukan buya acikin jini ko wuri me danshi kamar farjin mace ko mahaifa  ahankali xasuna yad'uwa. shi yasa akeso da zarar kaji wani alamu kamar:

zafin saduwa, rashin haihuwa, kaikayi, kuraje, fitar farin ruwa ko dorowa dorowa, ko 6arin ciki, ko jin tsira kasan nono na hagun ko dama, ko jin motsi a mara ko wasa na al ada samuwar ciki vayan mahaifa dss jin daya daga cikan alamun nan na nuni da ciwon sanyi. se ka garzaya asibiti ko kemis domin duba lafiyarka in kuma bakaje ba to zaka gamu da matsala gaba Allah kyauta.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Dan allah inafama da infection inasun magani

    ReplyDelete
Previous Post Next Post