NASIHOHI AKAN WATAN AZUMIN RAMADAN. !!

Sheikh Adamu Tsoho Jos A lokacin da yake jawabi a wajen Mauludin Imam Mahdi (As).


Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates. Tare da wakilinsu --Idishia Jos.

     Watan Ramadan wata ne da ake so mutum ya kara zage dantse, yayi damara na ibada, domin Azumi Allah (T) ya sanya shi fa'ida ga mutane da al'umma. Kamar yadda muka sani cewa kowacce ibada da ibadoji da Allah ya wajabta akan mu kamar Azumi, Sallah, Hajji, Zakka da sadar da zumunci da sauran ayyuka na ibada duka suna da fa'ida ga rayuwan mutum da kuma alakansa da al'umma. Bayan kasantuwan  tsayuwa da takalifin abinda ya ratayu akansa na bautan Allah (T) to kuma akwai fa'ida wanda yake shi mutum zai samu sakamakon abinda ya tsayu dashi na ibada.

Dan haka shi Azumi ba kawai mujarrabin kame baki bane daga rashin cin abinci ko rashin sha ko jima'i, a'a Allah (T) ya sanya Azumi ya zamo kariya ne gashi mutum daga dukkan abinda yake haram ga mutum. Haram a wajen magana, haram a wajen aiki haram a wajen mu'amala. Shi yasa ma yazo a hadisi Manzon Allah (S) yake cewa; Mafi karancin abinda Allah (T) ya farlanta akan me azumi a cikin azuminsa shine barin cin abinci da abin sha, shine kadan daga abinda aka farlantawa mutum. Amma abubuwan da aka farlanta ko aka wajabta maka a lokacin da kake ko ka samu yana da yawan gaske.

Shi Azumi ba aiki ne na yankewa daga barin cin abinci da abin sha ba kawai, Azumi yana sa mutum ya zamo kamamme daga abinda yake haram daga zuciyarsa da aikin sa, Allah ya saka mana Azumi don mutum ya zama yana da karfafuwan imani a zuciyar bawa sannan zuciyar ta tsayu ta ginu akan tarbiya na kyawawan dabi'u. Tarbiya wajen magana da mu'amala da tarbiyan zuciya. Azumi makaranta ne na tarbiyan zuciya, ita zuviya ya zamo  ta samu kamala cikekke a dukkan janibobi na rayuwa ana so ya zama duk mai azumi ya zamo ya samu wannan fa'idodi.

Domin Babban makasudi na musulunci shine canza mutum, Allah (T) ya aiko da Annabawa domin su canza dan Adam a bisa mummunan rayuwa da dabi'a mummuna zuwa ga dabi'a wacce take tsarkakakkiya rayuwa wacce take tsarkakakkiya. To kuma canza mutum ba zai yuwu ba sai ta hangar ayyuka da zai tsayu dashi. Shi yasa Allah (T) ya aiko mana da Annabawa suka zo mana da dokoki da ka'idodi na rayuwa, aka farlanta mana wasu ka'idodi na rayuwa. Wanda kuma duk abinda Allah farlanta mana na ibada to amfanin abin yana komawa ga kammune.

Shi yasa musulunci addini ne da yake nufin ya gyara shi mutum da al'ummasa. To kuma ba za'a iya gyara mutum ba sai an gyara zuciyarshi, duk lokacin da zuciya ta gyaru zuciya ta samu kamala a cikin dabi'unsa da halayensa to zaka ga mutum ne zai gyaru, mutum ne zai samu kamala, da dabi'unsa da halayensa. To idan kuwa aka samu daidaikun mutane daga cikin al'umma sun gyaru to kaga al'umman kenan zata gyaru. Kamar yadda Allah (T) yake cewa; Allah (T) baya canzawa mutane halinda suke ciki har sai sun canzawa kawukansu. To musulunci yana kokarin canza shi mutum ne.
Sheikh Adamu Tsoho Jos a lokacin da yake yanka Cake na Murnan Haihuwan Imam Mahdi (AJT).

To daga cikin hanyoyin da Allah (T) yasa na canza shi dan Adam na canza rayuwan mutum musamman ma mumini shine akwai azumi, domin manufar azumi yakan canza rayuwan ka. Shi yasa idan watan azumi ya kama to zaka ga rayuwan al'umma musulmi takan canza rayuwan mutane a daidai ku ya kan canza, akan shiga wani yanayi ne saboda anshiga wata na rahama wata na ibada wanda zakaga ana shagaltuwa da wasu ibadodi na musamman. Shiyasa ake so a watan Ramadan an yawaita ibada mutum ya kara zage dantse shi ya kara damara a cikin wannan wata na Ramadan. Allah (T) yana girmama wannan wata na Ramadan shine an saukar da Alkur'ani a cikinsa.

Shiyasa ma idan watan Ramadan ya kama zakaga an dukufa da karanta Alkur'ani, a gidane ne a makarantu ne da ko'ina. Yazo a ruwayan hadisi daga imam Jafar Assadiq (As)  yana cewa; An saukar da attaura a ranar 6 ga watan Ramadan, Injila kuma ansaukar dashi a ranar 12 ga watan Ramadan, Zabura kuma an saukar da ita 18 ga watan Ramadan, shi kuma Alkur'ani an saukar dashi a daren Lailatul Qadar. Wannan yana nuna mana Karin girma da muhimmancin nashi watan Ramadan, wanda na wata  bane na wasa ko na bacci ko wargi ko wani abu makamancin haka ba.

Yazo a cikin hadisin daga Abi-Basir An Abi-Abdallah (As) yana cewa; Manzon Allah (S) ya kasance idan Goman karshe ya shiga to sai ya zage dantse shi, kuma a lokacin yakan nisanci matansa yakan raya dare da ibada yakan shagaltu ne da ibadodi a goma karshe. Shi yasa ma ya zamo yakan shiga Ittikafi a wannan lokacin din. Kaga duk wannan ruwayoyi ne da yake da mahimmanci kara damara musamman ma a cikin watan Ramadan. A wani ruwayan hadisi daga Ahmad Bin Muhammad Alkufi An Aliyu Bin Hassan Bin Aliyu Bin Fadal An Abihi An Aliyu Bin Musal-Rida An Aba Ihi (As) yana cewa; Manzon Allah (S) yana cewa; Lallai watan Ramadan watane mai girma Allah yana ninninka  ladan kyawawan aiyuka a ciki, kuma Allah yana shafe munanan ayyuka a ciki. Shi yasa watan Ramadan wata ne da ake ninnika kawawan ayyuka, kuma ana shafe zunubai a cikinsa gwargwadon imanin ka gwargwadon aikin ka.

Insha Allah zamu cigaba a kashi na Biyu.
#FreeZakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post