NASIHA ZUWA GA MASU KIRAN KANSU 'YAN MEDIA.DA WAKILCIN DA SUKE YI WA HARKA. (1}

NASIHA ZUWA GA MASU KIRAN KANSU 'YAN MEDIA.DA WAKILCIN DA SUKE YI WA HARKA. (1}
-----------
Nasir Isa Ali
---------------------
Da farko dai,Allah ta'ala yana cewar "da ji da gani da sauraro duk cikarsu ababen yiwa tambaya ne...
Kar da mutun ya dauka cewar domin waya ko kwamfutar dake hannunsa tasa ce,don haka bari ya rubuta abinda ya ga dama ya watsa wa duniya, a'a kamata ya yi ya san cewar,masu karanta rubutun nasa suna da yawa matuka,kuma suna da bambanci ra'ayi,ilimi,fahimta da hange. Kuma zasu iya tasirantuwa da abin da hannayensa suke rubutawa.

-
Wata rana muna zaune kusa da shaikh Turi (RTA) za'a sha ruwa (ranar alhamis ne) to shaikh ya dauko Tufah zai ci,sai ya ga walkiyar haske a bayansa da ya juya sai yaga ashe wani ne yake ta kokarin daukar su hoto.
Sai shaikh yayi sauri ya dakatar da shi,sai yayi tambayar cewar "shin komai ake dauka a saka a MEDIA ne? Sai ya kallo ni yana murmushi. Sai nace masa 'Afuwan ya shaikh' sai yace min 'La ba'as'
Sai nace wa mai daukar hoton ya dakata,kuma kar ya dora hoton da ya dauka a MEDIA,Allahumma sai dai in rubutun nasa ya dace da hoton,ko kuma yanayin ya bada damar haska hoton ga duniya
-
Yan MEDIAN nan namu zai yi wahalar gaske ka gansu suna rubuta matsalolin su ko na gidajensu suna yada wa duniya,kuma ba wai basu da ita matsalar bane a'a ba zasu rubuta ta bane saboda tsabagen iya boye sirinsu ne yasa ba zasu taba rubuta mana matsalolin nasu a DEDIA ba.
Misali,ban taba ganin wani dan MEDIAN ya rubuta mana cewar "matarsa tayi yaji saboda ya kasa ciyar da ita ba. Haka zalika ba zai taba rubuta cewar,an Koreshi daga gidan haya saboda ya kasa biyan kudin hayar ba.  In ma ta kama ya fada wa daidaikun yan'uwa domin a tallafa masa,to zai lankwaya ne ya juyar da maganar da cewar,ai mai gidan nasa dan izala ne shiyasa ya uzzura masa saboda bambancin aqida.da dai sauransu zantuka.
-
Haka zalika ba zai taba rubuta mana'Labarai da Duminsa" Yau an koro min yarana daga makaranta saboda na kasa biyan kudin karatunsu ba. Haka ba zai taba rubuta cewar 'dansa ko 'yarsa sun fandare masa ba da sauran munanan ayyukansa a MEDIA ba.
Amma duk kankantar matsalar dake cikin yan'uwa ko Harka to yanzu zai dauko ya kawo MEDIA don kawai ace ya iya samo sirrin Yan'uwa ko sirrin Harka.
Ko kuma ace shi kwararren dan MEDIA ne.
-
Aikin MEDIA aiki ne na Ilimi,basira,fasaha da matukar hangen nesa,domin kana magana ne da miliyoyin mutanen duniya,wanda wasu suna iya shiriya sakamakon aikinka. Haka kuma kana iya karkatar da miliyoyin mutane sakamakon aiyukanka na MEDIA.
Don haka yadda muke ganin dacewar boye sirrikan mu da na iyalin mu da na ofisoshin mu,to ya zama tilas mu boye sirrin Harka Islamiyya da sirrikan yan'uwa domin kare martaba da girman ita Harka din.
Sai mun hadu a kashi na biyu.
-------
Nasir Isa Ali
----------------------
Juma'at Kareem.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post