Nakan rubuta Waka Amma banida kudin fitar da ita sai dai in aje sannan a baya lokacin kaset mai zare muna buga waka mu gurza mu sayar sai ya zama yanzu zamani yazo da memori da Ka bari wani ya samu to ta fita hannuka."

Firarmu da fitaccen mawakin nan wanda yazo na daya a gasar mawakan harkar musulunci  Aminu mai Falala katsina gasar da aka gabatar shekarar data gabata.
Lokacin da wakilimu Salisu Umar mazaje ke masa tambayar a garin katsina

Lokacin da wakilimu Salisu Umar mazaje ke masa tambayoyin a office dinmu a garin katsina

Daga shafin Ma'asumah Nigeria News Updat a cikin Shirin mu na (FILIN MAWAKA)
*----------------------------------------------------
Ma'asumiyya: Masu sauraron mu zasu so sanin dawa muke tare a wannan lokacin tare da dan takaitaccen tarihinka?
.
Aminu Mai Falala: "Sunana Aminu Maharazu ana yimin lakabi da Mai falala,
Kuma an haifenine a cikin garin katsina a unguwar Tudun wada a shekarar 1979,
Nayi karatun Primary a fodiya Katsina daga nan kuma nayi Government Pilot Secondary School Katsina daga baya kuma naje Dan fodio college of Arabic and Islamic studies nayi diploma a harshen larabci wannan shine a tkaice."
.
Ma'asumiyya: Shin yanzu kakai shekara nawa da fara waqa?
.
Aminu Mai Fala: "Zan iya hasashen hakikaba, zan kai shekaru kamar shekaru 20 tun ina dalibi a fodiya."
.
Ma'asumiyya: A kalla yanzu waqoqinka sunkai nawa?
.
Aminu Mai Falala: "To inada wakokin da na rubuta su sukafi yawa amma ban buga a studio ba wadanda na buga kuma na fitar zasu kai 20, a kalla."
.
Ma'asumiyya: Minene yaja hankalinka ko nace minene silar fara waqar ka?
.
Aminu Mai Falala: "Da yake ita waka dabi'ace wato (nature) kawai na tashine naji inayi sai dai magabatan mu a wannan fagen Sune kashin bayan samun duk wata nasara dana samu."
.
Ma'asumiyya: Kusan dukkan wani abu na rayuwa ana samun kalubale musamman bangaren waqa shin ta bangarenka wanne kalubale ka fiskanta?
.

Aminu Mai Falala: "Gaskiya yanda yawa wasu sun gabata wasu kuma har yau kirkira waka da rubutata ba matasala bane nidai a gurina Alhamdulillah amma nakan rubuta yazama banida kudin fitar da ita sai dai in aje sannan a baya lokacin kaset mai zare muna buga waka mu gurza mu sayar sai ya zama yanzu zamani yazo da memori da Ka bari wani ya samu to ta fita hannuka."

.
Ma'asumiyya: Kana nufin yanzu an samu cigabane amma ta wani bangaren an samu nakasu kenam?
.
Aminu Mai Fala: "Za'a iya fadar hakan tunda komai yakanzo da amfani da kuma rashin amfani."
.
Ma: Watannin baya da suka gabata anyi gasar waqa akan Imam Hassan Wanne yanayi katsinci kanka a wannan lokacin sakamakon kasancewarka zakara a wannan gasa?
.
Aminu Mai Falala: "Gaskiya ba zan iya misaltawaba nayi farin cikin da ban taba yin irinsaba a rayuwata koda yake nayi wani irinsa daga baya."
.
Ma'asumiyya: Ko zamu iya sanin wannene kayi irinsa a bayan?
.
Aminu Mai Falala: "Dadin da naji irin na ranar da Nazo na 1a wannan gasar shine kyautar da na samu sakamakon wannan nasara shine zuwa ziyarar manzon Allah a birnin MADINA kuma cikin ikon Allah naje har na dawo wannan shine farin cikin da yafima farin cikin da naji yayin da aka ayyanani a matsayin na 1a ranar da mukayi gasar."
.
Ma'asumiyya: A sanadin Wannan gasar sunanka yakai inda bakajeba ko nace ba kayi zatoba shin ko kasamu wata sabuwar mu'amala da jama'a sabanin yanda kake a baya?
.
Aminu Mai Falala: "Hakane baya ga karamcin ziyara kuma na sami karamci daga masoya ahalil-baiti (as) daga mutane daban daban kusan ko yaushe ina samun sakon taya murna da fatan al'khairi da kyautuka daga masoya manzo da iyalan gidansa tsarkaka (as)."
.
Ma'asumiyya: Kusan yanzu muna cikin wani yanayi marar dadi da ya ratsa cikin harkarnan tun daga bayan Waqi'r nan na rarrabuwa har abun ya fara shafar mawaqanmu minene shawararka gasu mawaqan?
.
Aminu Mai Falala: "Har kullun ita matasala abokiyar tafiyace shawarata ga mawaka da suyi riko da jagoranci musamman a bangarenmu na ittihadu munada jagoranci mai inganci Alhamdulillah muhada kai domin yima wannan harka aiki da taimakon jagoranmu akan isarda sakonsa a ko'ina."
.
Ma'asumiyya: Kayi waqoqi shin a cikin waqoqinka ko kana da bakandamiyya?
.
Aminu Mai Falala: Ba haushe idan yace bakan damiya wato wadda tafi kowace in kana nufin haka gaskiya kai tsaye bazan iya cewa gataba amma wadda akafi sanina da ita a wannan zamanin waken imamu Hassan Al Mujtaba (as)
.
Ma'asumiyya: To ko zaka dan bamu ko wasu daga cikin Baitukanta?
.
Aminu Mai Falala: " 1. -Wanene imam HAssan wata kila wani yayi tambaya,
-Ba boyayye bane ga mutanen yau da mutanen jiya,
-Jikane shi gurin manzona khairil anbiya,
-Dan fatmane diya ta rasulu da sayyidina Ali maulana.
2. -Shine farko cikin dukkan jikokin annabi
a cikin lakabinsama da akwai lakabin sibdinnaby,
-Farkon Dan Fatima da Ali dan abi dalibi,
-Kuma an haifeshine shabiyar ga wata mai darraja ramadana.
3. -Shekaru biyu Anka haifi imamu a bayan hijjira,
-Kuma ranar lahadi a ruwayar da tafi shahara,
-A gari mai darraja na rasulu MADINA munawwara,
-Kuma ranar haifuwa tasa manzo yayi farin ciki yai murna.
Alhamdulillah,
.
: Me zakace game da wannan shafin namu ta bangaren shawara ko karfafawa?
.
Aminu Mai Falala: "A gaskiya wannan shafi yananda muhimmanci sosai shawarata ga masu gudanar dashi shine sukara kaimi da kuma tattaro abubuwa masu muhimmanci musamman Isar da sakon harka islamiya da abinda ya shafi harkar kanta insha Allah."
.
Ma'asumiyya: A karshe ko akwai wani abu ko sako da kake san isarwa wanda bamu tambaya ba?
.
Aminu Mai Falala: "A Karshe ina godiya ga wannan shafi da fatan Allah ya kara tai mako da jagoranci bihakki Muhammad Wa Ali muhammad."
.
Ma'asumiyya: Mun gode da lokacinka garemu.
.
Aminu Mai Falala: "Nima nagode."
.
Daga
Ma'asumiyya Nigerian News Update
Tare da Wakilinmu
Salisu Umar Mazaje
09021381323

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post