_JAGORAN GASKIYA_
__Sayyid Zakzaky (h) [Jagoran Gaskiya]
Ta yiwu wani ya ce; ehen, ai ba kowa bane Musulmi a qasar nan, sai mu ce masa; eh, dama can ba kowa bane Musulmi lokacin da ake yin Musuluncin kafin Bature ya zo ba, wa ya ce maka sai kowa ya zama Musulmi ake Musulunci? Su Musulmi za su tsaya akan addininsu, da kishin addininsu, da tsarin addininsu, wanda ba Musulmi ba kuma ya yi nasa addinin.
Ya wuce haka nan? Wa ya ce maka idan za a hadu da wanda ba Musulmi ba, dole musulmi ya ajiye Musuluncinsa? Ba kowa na da haqqi ba? Ina da tambaya. Yana daga cikin haqqin wanda ba Musulmi ba, Musulmi ya fasa Musulunci? Mun ce ka da wani ya yi wani addini daban? To, mun ce ka da Kirista ya yi Kiristanci? Ba haqqinmu ba ne.
Mu ba mu ce ka da Kirista ya yi Kiristanci ba, ya yi Kiristancinsa. Ya za a yi ya zama haqqinsa ne ya yi nasa, amma namu haqqin shi ne mu fasa namu? Muna da namu yana da nasa. Tana yiwuwa ka ce; ehen, amma ai ka ce addininku ne zai yi iko, sai mu ce; eh, me zai hana kuwa? Dama addininmu ya gaji ya yi ikon ne ai, a tsarin iko yake dama. Shi me addinin Kiristanci ba ruwan shi da iko.
Shi ana yin addu’a ne a Coci ranar Lahadi, to ba za mu hana addu’a ba, a je kowanne Coci a yi ta addu’a.
Amma mu addininmu shari’a ne, da qa’ida, da rayuwa ma
gaba daya. Addininmu al’adunmu na ciki, siyasar mu na ciki. Manzon Allah shugaba ne wanda wajibi ne a yi masa biyayya.
Kuma Manzon Allah idan ya ajiye Khalifa dole a bi Khalifa din.
Saboda haka mu a wurinmu shugabanci Khalifcin Allah ne, ba wani wanda yake da iko ya dauki shugabancin al’umma ya sarrafa al’umma din idan ba Hujja daga wajen Allah ba, saboda su al’umma din halittar Allah ne, kayan Allah ne.
Kamar yadda mutum ba zai sarrafa dukiya yadda ya ga dama ba sai bisa qa’ida, haka ma mutum ba zai iya mallakar al’umma ya sa musu doka ya ce musu; ku yi ko ku bari ba sai da izini daga wajen Allah. Kun ga mu a wurinmu shugabanci, Halifcin Allah ne.
Da wannan ina iya ce muku yanzu ba a sarari yake ba, da can shugabanci a qasar nan Halifcin Allah ne tun bayan jihadin Shehu dan Fodiye? Bayan da Bature ya ci qasar nan da yaqi, shugabanci ya zama Halifcin wane? Idan ba ka sani ba aqalla Gwamna babba Halifan wane ne? Halifan Sarkin Ingila ne, to shi Sarkin Ingila Halifan Allah ne? Halifan wane ne? Halifan Shaidan ne! To Halifcin Shaidan za mu bi ko Halifcin Allah?
Kuma ka da ka ce min ‘yanci ne, wai an samu ‘yanci, tsarin bai canza ba, nizamin da ke iko shi ne, abin da Bature ya kafa shi ne har yanzu ba sake.
To tana iya yiwuwa mutum ya ce min; idan haka nan ne ai an nuna bambancin addini, kuma an hana wani ‘yanci, sai mu ce; a’a, bilhasali ma dai idan mun yi haka nan ma mun ma dace da irin tunaninka na dimukradiyya. Ba kana son a yi dimukradiyya ba? Tambaya; mece ce dimukradiyya? Amsa;
dimukradiyya ita ce mulkin masu rinyaje da kiyaye haqqinmarassa rinyaje ‘full stop’. Idan haka nan ne idan Musulmi suka kafa nizamin su ya yi iko an haqqakar da wannan, don dama Musulmi suka fi yawa, kuma addinin su zai yi iko, kuma addinin Musulunci akwai kare haqqin wanda yake ba Musulmi ba, ka ga an yi dimukradiyyar da kake so.
Kuma kowa yanzu ya miqe, sai ya ce; zama lafiya, zama lafiya, a zauna laafiyaaaa, To, sai mu ce; Musuluncin ma, ma’anar ‘Islam’ zamaa laafiya ne! Ka ga ba an yi ba kenan? Sai dai abu daya za ka ce min; Ba ka son addinin Musulunci kawai!
Amma ba ka da abin da ya yi daidai da Musulunci!Ta yiwu ka ce; idan haka nan ne ai Amerika ba ta son Musulunci, saboda haka za ta kawo mana hari, sai mu ce maka; to ta kawo! Domin muna batun bin Allah ne, har wanda yake tare da Allah ya ji tsoron wani? To ballantana duk bayan wannan, idan kai rayuwar duniya kawai ya bude maka ido, ka ga za a samu muradinka, ka ga za a samu zama lafiya, za a samu mutanen da ake alfahari da su, za a samu masu qumaji da masu ilimi, duk dai abin da kake so za a samu. Sai kuma mu ce maka ballantana kuma akwai wani abu guda; mu gare mu Musulmi ba hadafinmu rayuwa a duniya ba ne kawai, mu a wurinmu rayuwar duniya wasila ce ta zuwa lahira, wato hanya ce ta zuwa rayuwar lahira.
Domin Allah Ta’ala bai shirya dan adam don
(dauwamammiyar) rayuwa a wannan doron qasar ba. Ko ba komai muna ganin ana mana dauki dai-dai, ana mutuwa dai-dai dadai-dai, kuma dai duk za mu marmace, kuma wata rana dai Allah zai kawo qarshen duniyar ma gaba daya. Komai da ka ke gani ya wargaje ‘Kullu man Alaiha Faan’. Allah ya tarwatsa duniyar ma gaba daya ya rugurguza ta, ya kece sama ya rubdo
da Taurari da Wata da Rana, a kece su a mutsuttsuka a maisheta gari, a baje ba tudu ba kwari. Duniya ta zama bai daya, sannan a taso da matattu daga mace, a yi hisabi, kuma akwai makoma wuta ko Aljanna. Amma kuma ran nan ba abin da ke amfani “Yauma la Yanfa’u Malun wala Banun, illa man Atallaha bi Qalbin Saleem.’
Wannan ‘Islam’ din nan da ka ji din nan shi ne kuma mafita ran nan. To da me muka manta don Allah? Idan ka yi Musulunci a nan, mu zauna lafiya, mu samu ci gaba da walwala da jindadin rayuwa, mu sami izza, mu yi tinqaho da cewa; mu ne, qasar mu ce, kayanmu mu ne, al’umma Musulma, sannan kuma gobe mu je ga Allah, ya ce; barkanku da zuwa, ga abin da na yi muku tanadi (na Aljanna).
Ko (mu zabi) wannan, ko (kuma mu zabi) dayan, wato qasqanci da rayuwar wulaqanci a duniya, irin wanda yanzu muke ciki, ba izza a tare da mu, kullum muna nan muna tiqi, muna yiwa wadansu bauta, kuma ba sa godewa, ba su taba yabonmu ba, kullum sunanmu baqaqe. Kullum sai balbalo mana bala’i suke yi, ko Talabijin ka bude ba ka jin kyakkyawar magana dangane da mu, sai yunwa da cutar qanjamau, su suka qirqiro qanjamansu, amma sun ce; wai namu ne. Da an ce qanjamau, sai a yi ta nuna baqaqen mutane, wai sune da qanjamau, da yunwa, da yaqi, da fatara, da talauci, da cututtuka!
Sanqarau, Qarambau, Qanjamau, Gudawa da Amai, duk Afrikane! Yaqi, kashe-kashe, ba su da wani magana dangane da mu banda sharri! Su ci arziqinmu, su talauta mu, su balbalo mana bala’i, a rayu a wulaqance!Wata rana na taba zuwa Abuja neman Biza, sai na ji wadansu ‘yan Nijeriya suna tattaunawa, suna cewa; ka sha wahala, a yi ta maka tambayoyi, a yi ta maka tsawa, ka sayi
tikiti da kudinka, ka dibi kudin guzuri da kanka, ka je (Turai), amma ba wanda zai ce maka marhaban ko sannu. Ka kashe kudin ka dawo haka nan, ko sannu ba wanda zai ce maka ballemarhaban.
To ka ga kadan kenan, rayuwa cikin wulaqanci da qasqanci da wahala, sannan kuma dama shi kenan, idan ka ji‘Kizyin fil Hayatid-Dunya,’ to ka saurari ‘Ashaddul Azaab’ a ranar Alqiyama.
Za ka ga duk inda ka gani a Alqur’ani Allah Ta’ala yana bayanin azaba, za ka ga yana cewa; zai dandana musu kunyata a rayuwar duniya, da kuma azaba dawwamamme a lahira. ‘Azabil Muqeem.’ Nan a samu ‘Khizyi’, kunyata, gobe qiyama a samu azaba. To yanzu Allah ya kiyaye mana na qiyama, ba mu ganshi ba, amma yanzu a nan me muke gani? Ba mu ganin ‘Khizyi’, ba mu ganin kunyata da qasqanta da wulaqanci? To me kuma ya rage mana? Allah ya sauwaqe mana ‘Azabil Akhira’ kuma.
_______________________________________
[Jawabin Sayyid Zakzaky (h) data Littafin ""MuLKIN MALLAKAR TURAWA""]
Wakilinmu,
Mahadi Tukur Almizan
[Al-Muntaxarul-Mahadi ___Tukur__Amizan] aikinmu
MUSULUNCI HANYAR RAYUWA CE GABA DAYA