Photon Mahaifiyar wakiliyar mu Shaheedat Mujahidat yolawy kenan margyayiya Hauwa'u Adam wadda ta rasu yau da safe illahy ya jikanta ya gafarta mata. |
Daga Shafin Ma'asumah Nigeria News Updated
Tare da Wakilin mu Sadar Yusuf Kano.
Gundumemen aiki mafi girma kuma mafi muhimmanci da zaka aiwatar a wannan harka shine: *Ka gyara kanka ka zama mutumin kirki wanda za'a kalla ace wannan mutum ne na gari wanda ya siffantu da addini sahihi da kuma salimiyar mu'amala*.
Da ace 'yan uwa zasu kubuta daga sharrin wannan harshen naka dake cikin bakin ka Tom ka cancanci jinjina kuma baza mu gajiya ba wajen yi maka godiya tare da karfafa sauran 'yan uwa suyi koyi da halayen ka.
Da yawa 'yan uwa sun zama mazlumai a hannun sauran 'yan uwa ta hanyar yada zancen karya da kifce a kansu, wanda hakan ke zaman wani babbar barazana ga sihhar 'yan uwa da yawa masu kokari gami da neman hanyar cigaba ga wannan harka din.
Shin me yasa ba'alin 'yan uwa zasu zama azaba mai radadi ga wani ba'alin na 'yan uwa?
Idan akayi maka laifi ka hakura hakan gazawa ne ko jarumta ne?
Hakura da cutawar mutane yana alamta cikar kamala ne ko yana nuna rashin kimanta kai?
Yardar Allah ta'ala kake nema ko ta mutane?
'Yan uwa mu daina yaudarar kanmu son zuciya ne ke dawainiya damu kuma idan bamuyi da gaske muka yake ta ba zata kaimu haddin fadawa wani wawakeken rami wanda nake hango shi a gaba kadan.
Domin kaucewa wancan rami dole mu gyara, ko kuma tun wuri ma mu sanar da wancan mukhlisin dattijo cewa dama baza mu iya ba saboda haka ko ya nemi wasu ko yasan abinyi.
Eh da gaske ne kuma kar kaji wai da wani ake, a'a da kai nake kai din mai karanta wannan rubutun, DOLE KA GYARA!
DOLE KA GYARA!!
DOLE KA GYARA!!!
Bissalam.
Tags:
Tunatarwa