LIYAFAR UBANGIJI A WATAN AZUMIN RAMADANA.

              Taskar Sheikh Adamu Tsoho Jos.

Kada mu ai'kata munanan ai'yuka a cikin wannan wata Mai Girma, kamar su Gulma, har idan mun ga wani zai yi gulma ! Ko cin
mutuncin MUSULMI, to, mu hana shi yin haka. Mu ce masa: "Lalle mu munyi alkawarin cewa zamu nisanci ai'yuka na haram a cikin wannan
wata. "HAR idan Bamu iya Hana shi yin gulma ba ko cin mutuncin MUSULMI, to mu tashi daga wurin, mu kaurace masa.

Saboda ya kamata MUSULMI su samu aminci daga wurin mu.Duk Wanda bai amintar da MUSULMI daga sharrin hanun sa da na bakin sa ba,da kuma sharrin idon sa ba, to a hakika shi ba MUSULMI bane.Shi kawai MUSULMI ne a zahiri, kamar Wanda yake cewa: "Na shaida BABU wani UBANGIJI sai Allah," amma kuma bai lizimci abin da ta kun sa ba. Imam Ja'afar Safik(as) yace:" Manzon Allah(sawa) yace: Bana baku labari saboda me yasa ake ce wa mumini, mumini ba ?Saboda amintar da mutane da yake yi akan dukiyar su da rayukan su. Bana Baku
Kabarin wane ne MUSULMI ba ?Musulmi shine Wanda ya kubutar da mutane daga sharrin hanun sa da na bakin sa.

Ku sani fa ! Har idan zaku iya wulakanta wani musulmi, ( Allah ya tsare mu ) ko kuma kuyi gulmar sa, ko ku ci mutuncin sa! to ku sani za kuyi HAKAN ne acikin FARFAJIYAN Allah Ta'ala (Watan Ramadana Mai daraja) watan da aka Kira ku zuwa LIYAFA ta musamman a FADAR Allah Madaukakin Sarki. Kuma kuna kan teburin Liyafa ne ! Don haka ya kamata mu San cewa mu bakin Allah Ta'ala ne acikin Watan Ramadana ! To, kuma duk da muna gaban Allah Ta'ala zamu nuna rashin ladabi da girmamawa ga bayin Allah !!! ?.

Lalle wulakanta bawan Allah, wulakanta Allah ne !!!. Mutane fa sune bayin Allah, musamman idan sun kasance Akan tafarki na Imani da ILIMI da Takawa. Kada ku kaskantar da zunubi ko yaya,saboda karshen sa na da hadari!. Domin mutumin da yake yawan sabo ,har yakai matsayin da ya zama masa jiki da dabi'a, to zai iya yiwuwa a lokacin mutuwar sa ya karyata Allah Ta'ala ,ya karyata ayoyin sa. Allah Ta'ala yace: ".....sannan karshen Wanda suka munana ai'yukan su, shine su karyata ayoyin Allah, kuma daman sun kasance masu izgili da ita (ayoyin Allah)."

Wannan itace mummunan saka mako mai halakarwa, wacce ba alokaci daya ake kaiwa ga ita ba, a'a a Hankali, a Hankali ake KAIWA ga wannan mummunan karshe!!! .Kallon Haram a nan,da yin gulma a can, wulakanta MUSULMI a wani wurin ,da mummuna mu'amala da dan'uwanka, ko abokin zaman ka.Dukkan wadannan zunubai suna tsirowa ne su girma a zuciyar mutum a hankali a hankali,Har su
mamaye ZUCIYA ,su Mai da ita Baka Kirin ko wuluk Mai tsananin duhu.

 Sannan su shiga tsakanin mutum da SANIN Allah, HAR al'amarin ya kai mutum yayi musun tabbatattun al'amura na imani, sannan daga karshe ya karyata a yoyin Allah Ta'ala .Don haka ya zama wajibi da mu nisanci duk wani sabo acikin wannan wata Mai daraja da alfarma, kamar ,karya ,hikidu,Hassada ,da sauran su,don suna munana Ladubobin mu a gaban Wanda ya Kira mu zuwa ga Liyafa ta Girmamawa, wato Allah Madaukakin Sarki.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates tare  -Idishia Jos

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post