LAFIYA UWAR JIKI

WASU SINADARAN ABINCI MASU GINA JIKI:

(M.N.N.UPDATES) 

Da Harshen Hausa zamu iya cewa Mineral salts na nufin wasu sinadarai masu gina jiki wadanda ake samu a cikin kusan dukan nau'o'in abinci iri-iri wadanda muke ci yau da kullum  kamar ya'yan itatuwa,ruwa,madara,nama,gishiri musammam na miya wanda aka karawa wani sinadari mai suna Iodine a cikin sa da sauransu. Koda yake a wasu nau'o'in abinci ana samun irin wannan sinadari da yawa fiye da a wasu,amma akwai ire-iren wannan sinadarai a cikin abinci da dama wanda ake ci.

Amfanin wannan sinadari ga jiki

Suna taimakawa ruwan jiki gudana yadda ya kamata batare da shiga cikin aikin juna ba. Watau suna taimakawa wajen gudanar sinadarai da dama a jiki,kowanne kuma ya aikinsa yadda ya kamata,musamman sinadaran narkar da abinci na cikin ciki. Su na matukur amfani ga kowace kwayar halittar jiki watau sali da tsokoki da sauransu. A cikin wadannan sinadarai ne ake samun sinadaran tsayar da jini mai daga jiki, watau yayin da aka ji rauni.
Halitar kashi da hakora da ingancin su musamman a jiki,duk su na dogara ga ingancin wadannan sinadarai.

Wakilin Ma'asumah 🇳🇬Nigeria🇳🇬 News Updates.

@Auwal M. Tukur

   29/5/2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post