@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
Matuqar za ka bi dokar Allah, to, ba za kayi hasara ko aikin banza ba a rayuwarka.
Allah (T) ya wajabta mana azumin watan Ramadan, sa'an nan
ya gindaya mana wasu dokoki cikinsa wadanda za su inganta
mana shi tare da hana mana aikata abubuwan da za su bata
mana shi.
Bayan Allah ya shimfida mana dokokin sai kuma yace;
" KUMA KU CI KUMA KU SHA (cikin dare) HAR SAI FARIN
ZARE YA BAYYANA GARE KU DAGA BAQIN ZARE DAGA
ALFIJR (ketowarsa) , SA'AN NAN KU CIKA AZUMI (da rana)
ZUWA DARE..."
(Baqara, aya ta 187)
Wannan shine umarnin Allah (T) da ya yi mana, amma an
riwaito wani hadisi cikin Bukhari, in da yake cewa, Manzon
Allah (S.A.W.W) yace;
" MUTANE BA ZA SU GUSHE BA (suna cikin) ALKHAIRI,
MATUQAR SUNA GAGGAUTA (yin) BUDA BAKI."
(Bukhari, hadisi na 1957)
Idan muka nazarci ayar za mu ga cewa lalle Allah (T) bai
fayyace mana takamammen lokacin daren da yake nufi ba,
domin da farko dare, da gaskiyarsa da kuma qarshensa
dukkansu dare ne.
Cikin hadisin kuma sai Manzo (S) ya nuna mana cewa farkon
dare ne ba tsakiya ko qarshensa ba.
Jin haka kuma sai jama'a suka dimauta don gaggawa wajen
shan ruwa yayin Magrib kafin dare ya cika kamar yadda Allah
(T) ya umarce mu.
Wannan al'amari ya jefa mutane da yawa suna hasarar
azuminsu da sunan wai Sunnah suke aikatawa, alhali ba
Sunnah bace son zuciya ne.
Amma za mu iya fahintar gaskiya in muka nazarci wannan
hadisi na qasa wanda Iman Malik ya kawo daga Humaid Bn
Abdurrahman yace;
" LALLE UMAR BN KHADDAB DA USMAN BN AFFAN SUN
KASANCE (su biyun) SUNA YIN SALLAR MAGRIBA YAYIN DA
SUKE SAURARE ZUWA DUHUN DARE (yayi) KAFIN SU YI BUDA
BAKI, SA'AN NAN SUYI BUDA BAKI BAYAN (sunyi) SALLAH,
HAKAN KUMA YA KASANCE A RAMADAN NE (suke aikata
haka) ."
(Muwadda Malik, hadisi me lamba 638).
Idan mukan nazarci wannan hadisi za mu iya cewa Annabi (S)
shi ma bayan Magrib yake shan ruwa.