KISAN TA'ADDANCIN DA AKE A AREWA BABU WASU ALAMU NA KUSA KO NA NESA DA SUKE NUNA BUHARI ZAI MAGANCE MATSALAR.......!!!


...Umar Hassan Gololo...

Kullum sai an kashe Mutane,idan ba a kashe a Adamawa,ko
Borno ba to za a kashe a Yobe,kisan da ake ganin burin kawar
dashi ne ya karawa Buhari farin jini da daukaka a tsakanin
Mutanen Arewa,tun daga lokacin da Buhari Yayi alkawarin
kawar da Boko-Haram a cikin Watanni shidan farko na
mulkinsa har zuwa Yau ba a taba yin mako guda ba tare da jin
labarin ta'addancin Boko-Haram a birni ko kauye ba.

Abin kunya da takaici ga Buhari idan Yana da ita sune budewar
Kasuwar Barayin Shanu da Kidnappers a Arewa Maso
Yammacin Nigeria.
Shin Ina kwarewar tsofaffin Sojoji da'yansanda wadanda suke
tare da Buhari.? Shin Ina intelligence da strategies dinsu akan
Samar da tsaro.?

Ina amfanin register na layukan wayoyinmu da aka takura
Mana yinsa.? Ko Kidnappers ba da wayoyi suke amfani ba.?
Ina tracking devices din da kamfanonin layukan wayoyi suke
amfani dasu.?

Jiya an Kai hari an kashe Mata da Yara a Katsina,Yau an Kai
hari Sokoto Gobe Kuma Mutanen Zamfara ne suke jiran a
kawo musu nasu harin alhali Wai Gwamnatin da suka zaba
tana da Sojojin sama da kasa da Kuma 'yansanda, menene
amfaninsu.?

Wai maharan nan Kam bacewa suke yi ne.? Wadanda ake Kai
wa hari sun ce maharan suna tafiya da akalla babura sama da
dari Kuma kowane babur Yana dauke da Mutum Uku, idan sun
yi ta'addancin bacewa suke yi ne ko iska suke bi.?

Abin mamaki ne matuka ace sarkin Gargajiya ya fito ya
kalubalanci Shugaban Kasa akan tsaro
Ta'addancin Boko-Haram, Barayin Shanu da Kidnappers laifin
Buhari ne da Gwamnatin Buhari Kai tsaye babu boye-boye.

Dukkan Wanda Yake da Karfin hali yayi magana akan wannan
ta'addancin, Gwamnonin Jihohin Katsina da Zamfara sun yi
magana, Sarakunan Gargajiyar Zamfara da Katsina sun yi
magana, Masanan tsaro sun yi magana,amma Buhari Yayi
kunnen uwar shegu ya tsaya sauraron wasu tantirai wadanda
da zarar ya bar Fadar Aso-Rock ba zai sake ganinsu ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post