KAFFARAR AZUMI GA MARAR SA LAFIYA DAGA FATAWAR AYATULLAH SAYYID KHAMNE'I (R.A) !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TAMBAYA:- Shin, bayar da kudi gwargwadon mudu na abinci ga faqiri don ya sayi abincin da kansa (yayin kaffara) yana wadatarwa?
AMSA:- Idan har yana da nutsuwa kan cewa wannan faqirin zai wakilce shi ya sayi abincin da wannan kudi, daga baya ya mallaki abincin a matsayin kaffara, to, babu wata matsala ga hakan.
TAMBAYA:- Macen da aka dauke mata azumi saboda rashin lafiya, kuma ba ta sami damar rama azumin ba har watan azumi na gaba ya iso, to, a irin wannan hali shin kaffarar yana kanta ne ko kuma yana kan mijinta?
AMSA:- A irin wannan hali wajibi ne a kanta ta bada mudu na abinci a madadin kowacce rana, kuma hakan bai hau kan mijinta ba.
TAMBAYA:- Mutum ne yake da ramakon azumi na kwana goma, to, sai a rana ta ashirin na watan Sha'aban ya fara azumin, to, shin a irin wannan hali zai iya karya azumin da gangan kafin (Zawwali) ko kuma bayansa?
Kuma idan ya karya, shin, menene gwargwadon kaffararsa idan ya karya azumin kafin (Zawwali) ko kuma bayansa?
AMSA:- A irin wannan hali ba ya halatta ya karya azumi da gangan, to, amma idan ya karya da gangan kafin (Zawwali), to, babu kaffara a gare shi. Idan kuwa bayan (Zawwali) ne, to, kaffara ta hau kansa, wato ciyar da miskinai goma (10), idan kuwa hakan ya gagara, to, sai yayi azumin kwana uku (3).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
Tags:
Taskar ilimi