Ana sanar da 'yan'uwa cewa tun daga jiya Litinin ne 7/9/1440 wadda tai daidai da 13/5/2019, za a bude taron baje koli na Al-Qur'ani na Duniya a birnin Tehran, Iran. Kuma Alhamdu lillah, ta hanyar tuntubar Dakta Shuja'i Fard wakilin Jagora(H) a al'amuran kasashen waje da mas'ulan taron baje kolin suka yi, an samar da sashe na musamman da sunan Najeriya da Sheikh Zakzaky (H), daga cikin sashe-sashe 126 da taron ya kunsa, wanda za a baje kolin hotunan da suka shafi gwagwarmayar Jagoran, tarihin sa, Waki'ar Zaria da abin da ta haifar, da dai sauran su.
Sannan za a nuna hotuna na tarihin al'adun al'ummar Musulmi na koyon Al'qur'ni a Najeriya, karatun sa, haddar sa da yadda ake girmama shi a watan Azumi da sauran al'amuran tarihi da al'adu masu kyau don rayar da karantarwar Addinin Musulunci.
Don haka ana gayyatar duk wanda ke da sha'awar halarta daga jiya Litinin 13/4/2015, har zuwa tsawon kwanaki 10, daga karfe 5p.m na yamma zuwa 12a.m. na dare.
Ana bukatar duk wanda yake da wani littafi na Al-Qur'ani rubutun hannu, tarjamar Hausa ko wani littafi da aka rubuta na tarihin Harka da Jagora(H), da tarihin Shehu dan Fodiyo, da ko wane yare ya je da shi ko ya bayar aro akai, bayan taron za'a mayar masa.
Sannan an kebe ranar Alhamis 10 ga watan Ramadan wadda tai daidai da 16/5/2019, a matsayin ranar Shaikh Zakzakiy(H) da abinda ke faruwa a Najeriya. Taro ne na musamman wanda a can za a yi buda baki, kuma za a gabatar da jawabai a kan Maudu'ai daban-daban.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates --Idishia Jos.
Tags:
Labaran Duniya