HUKUNCIN YIN ALLURA GA ME AZUMI, DAGA FATAWAR AYATULLAH SAYYID KHAMNE'I (A.S) !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Ganin cece-ku-ce da matune ne ke yi, da kuma katsa-landan irin na masu shisshigi cikin addini da sunan malantaka yasa muka waiwaici fatawar Ayatul-Lahi Sayyid Khamne'i (R.A) don sanin haqiqanin hukuncin yin allura ga me azumi.
Da yawa za ka ji ana bada fatawar cewa yin allura da qarin ruwa ga me azumi yana karya masa azumin nasa, wasu kuma sukan ce ba ya karyawa.
Ga dai tambayar da aka yiwa Ayatul-Lah;
TAMBAYA:- Muna buqatar ka yi mana bayani kan hukuncin yin allura yayin da mutum yake cikin azumin watan Ramadan.
AMSA:- Babu wata matsala ga yin allura, sai dai in allurar ta kasance ta sanya wa marar lafiyan abinci ne, to, bisa Ihtiyadi wajibi ne a nisance ta yayin da ake azumi.
(Bisa wannan fatawa za mu iya fahintar cewa duk wata allura da za a yiwa me azumi matuqar ba ta kasance anyi ta ne a madadin abinci ba, to, babu wata matsala ga azumin me yinsa. Kuma da ma ai abinda ke karya azumi ya kasance abinda ya shiga ta hanyoyin qofofin jikin mutum, musamman ma ta maqogwaro).
Allah ya sa mu dace.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
Tags:
Tunatarwa