__Shaikh Saduq(R) ya ruwaito da Isnadi ‘Muktabari’ daga Imam Ali Bin Musa Ridha (AS) daga iyayensa daga Amirul-Muminin Ali (Alaihi wa ala Auladihis salam), ya ce; Manzan Allah (S) ya yi mana huduba wata rana ya ce;
“Ya ku mutane, ga watan Allah nan ya gabato muku da albarka da rahama da gafara. Wata ne wandaa wajen Allah (T) shi ya fi sauran watanni fifiko. Ranakunsa kuma sun fi sauran ranaku falala. Dararensa sun fi sauran darare falala.
Sa’o’insa sun fi sauran sa’o’i falala. Shi wata ne wanda aka kira ku izuwa liyafar Allah Ta’ala……
__Sharhi:_
Wato kamar liyafa shi ne, Allah Ta’ala ya kira ku ku zo ku ci abinci, ya shirya muku, ya jera abinci iri-iri. An kira ku liyafa, kamar ku baqin Allah ne a cikin watan Ramadan. An kira ku ya zuwa ga liyafar Allah. To, kuma an sa ku cikin ma’abota karamar Allah. Wato ma’anar wannan kiranku ya zuwa liyafar Allah, shi ne an sa muku wani lokaci da aka daukaka darajojinku. Aka ba ku damar samun lada azuminsa.Wato kenan kamar mutum ya je liyafa ya ci abinci, ya zazzabi abinci iri-iri masu dadi. Wannan kuma shi ne ainihin nau’o’in ibadodi da zikirori da sauransu, wanda za a dinga nunnunka ladanku.
“Numfarfashinku a cikin Ramadan tasbihi ne…..
Sharhi:
Wato lokacin da ka numfasa sai a rubuta maka kamar ka ce ‘Subahanallah’. Ka ga ko numfashin (da ka ke) yi ma idan kana barci ba ka sani ba (ana rubuta maka lada ne). Numfarfashinku tasbihi ne.
“Baccinku a cikin watannan ibada ne. Aikinku karvavve ne. Addu’arku abin amsawa ne. Saboda haka ku roqi Allah Ubangijinku da niyyoyi na gaskiya da kuma zukata tsarkaka. Ku roqe shi ya ba ku ‘Muwafaqa’ da azuminsa (azumin watan kenan), da farlanta Alqur’aninsa (littafinsa). Domin duk shaqiyyi shi ne wanda aka haramta ma gafarar Allah a wannan wata mai girma…..
Kuma a yayin yunwarku da qishinku a cikin watan nan, ku tuna da yunwa da qishin ranar Alqiyama. Kuma ku yi sadaka ga faqiranku da miskinanku. Kuma ku girmama tsofaffinku, ku ji tausayin yaranku, ku sada zumuncinku, ku kiyaye harsunanku, ku runtse idanunku daga abin da bai halatta ku gani ba, da kuma abin da bai halatta ku ji ba….
Sharhi:
Wato ku runtse idanunku daga abin da ganin ku bai kamata ya je gare shi ba, kuma ku kiyaye kunnuwanku daga abin da bai hallatta ku saurara da jin ku ba.
“Kuma ku tausayawa marayu na mutane, (hakan zai sa) Allah ya tausaya mana. Ku tuba ya zuwa ga Allah daga zunubbanku. Kuma ku daga hannuwanku da addu’o’i a lokutan sallolinku, domin (lokutan salloli) sune sa’o’in da suka fi falala, Allah (T) zai dube ku da Rahama….
Sharhi:
Allah yana duba ya zuwa ga bayinsa da Rahama kuma yana amsa musu in suka kira shi (wato in suka yi Munajati da shi), kuma yana amsa roqonsu in sun roqe shi.
“Ya ku mutane, rayukanku fa, jinginannu ne ya zuwa ayyukanku, saboda haka ku kame rayukanku da yin Istigfari. …..
Sharhi:
Wato an jingina rayukanku ga ayyukanku, kamar abin da muke ce ma; jingina. Jingina shi ne; ainihin ka je ka ba da wani abu sai ka biya wani abin da yake kanka ka karba. To, ranku kamar an ajiye ana jiran sai ka yi wani abu, ka qwato ran naka.
“Bayayyakin ku kuma dauke suke da nauyayyaki, ku sauqaqe nauyin da ke wuyayenku (na zunubai kenan) da tsawaita Sujjadodi. Ku sani cewa; Allah Ta’ala ya rantse da izzarsa, cewa; ba zai azabta masu yin sallah da sujjada ba, kuma ba zai firgita su da wuta ba a ranar Alqiyama (Yauma Yaqumun-nasu li-Rabbil Aalamin)….
“Ya ku mutane, wanda ya ciyar da mai azumi (Mumini) a wannan wata, yana da lada (a wajen Allah) daidai da ‘yanta wuya da gafara na duk zunubansa da suka wuce.
A ka ce; Ya Rasulallah! Ai ba kowane mumini yake da damar ya iya ciyar da masu azumi ba!”
Sai Manzan Allah (S) ya ce; “Ku ji tsoron wuta ko da da rabin Dabino ne.
Ku ji tsoron wuta (wato ku kiyaye kan ku daga wuta) ko da da kurbin ruwa ne…..
Sharhi:
Wato abin da za ka bayar ba lalai ya zama ya yawaita ba kenan, duk komai da kake da shi, komin qanqantarsa, ko da rabin dabino, in kana da dabinuwa guda daya, sai ka tsaga ka ba da rabi. Mai ya yi sauqin wannan? Haka ma aka ce ko da kurbin ruwa ne. Kurbin ruwa da tsagin dabino ko da wannan ne, ku yi qoqarin tseratar da kanku daga wutar Allah Ta’ala (da shi). Domin Allah Ta’ala yana ba da lada ga wanda ya yi wannan aiki qanqani, in bai samu ikon fiye da shi ba.
Mutum ne yake da ruwan da zai iya sha zai yi kurba uku sai ya ba wani kurbi daya. Ka ga ya ba da nawa kenan na abin da yake da shi? Sulusi. Kaga duk da yake kadan ne, amma ya kasa uku ya ba da kurbi daya, don haka ya bada da yawa.
Saboda haka yana da lada mai yawa. Dan abin da kake da shi shi ne aka ce ka bayar. Ba a ce sai kana da dukiya mai yawa za ka bayar ba. Abin da kake da shi ko ya qaranta, to dai ka bayar.
“Ya ku mutane, wanda ya kyautata halinsa (dabi’o’insa) a wannan watan, zai zama qetara gare shi akan siradi ranar da qafafuwa za su goggoce. Wanda ya sauqaqa ma wanda ya mallaka (wanda hannunsa ya mallaka), Allah zai sauqaqa masa hisabinsa…..
Sharhi:
Wannan yana nufin in mutum yana da bawa kenan, da watan Ramadan ya sauqaqe musu aiki (hidimomi). Na’am wani lokacin mutanenmu anan tunda yanzu ba bawa da ake siyowa a kasuwa, amma akwai hadimai, ko su ma mutane ne, za a sauqaqa musu ba sai a sa su wahala ba. Musamman su ma suna azumi ai, suna ji a jika.
Yawwa! To, saboda haka wanda ya sauqaqa ma wanda damansa ta mallaka, to, Allah zai sauqaqe masa hisabinsa.
“Wanda ya kiyaye sharrinsa na bakinsa da harshensa da idanunsa da kunnuwansa da qafafunsa da hannuwansa (ga mutane) a wannan watan, (kamar tsegunguma da gulma da tura masifofi ya zuwa ga mutane), to, shi kuma Allah zai kiyaye masa fushinsa ranar da zai gamu da shi….
“Wanda ya girmama maraya (ya kyautata ma maraya), Allah zai girmama shi ranar da zai gamu da shi. Wanda ya sada zumuncinsa, Allah zai sadar da shi da rahamarSa. Wanda kuma ya yanke zumuncinsa (a Ramadan), Allah zai yanke masa rahamarSa ranar da zai gamu da shi. Wanda ya yi ‘Tadawwa’i’ na sallah (wato sallar nafila kenan), za a rubuta mishi kubuta daga wuta. Wanda ya bada farali, yana da daidai da wanda ya bada farali 70 a wani wata ba a cikin Ramadan ba….
Sharhi:
Wato ba da farali a Ramadan yana daidai da ba da farali Saba’in a wani wata ba shiba. Kuma nafila bara’a ne daga wuta.
“Wanda ya yawaita Salati gareni, Allah zai nauyaya mizaninsa ranar da mizanoni za su yi rauni. Wanda ya karanta aya daya ta Alqur’ani zai zama ladarsa kamar wanda ya yi sauqar Alqur’ani ne gaba daya in ba a cikin wannan watan ba.
“Ya ku mutane, qofofin Aljanna a wannan wata (na Ramadan) budaddu ne.
Ku roqi Ubangijinku (kar ya rufe muku qofofinSa na Aljanna din). Kuma qofofin wuta (gidajen wuta kenan) rufaffu ne, ku roqi Ubangijinku kar ya bude muku su.
Shaidanu kuma za a daddaure su, ku roqi Ubangijinku ka da ya sallada su a kanku”.
__________________________
Ma'asuma Nigerian News Updates.
[Daga Littafin Ramadan da Ayyukansa]
Tareda Wakilinmu.
©__Mahadi Tukur Almizan.