HIJABI MUTUNCIN ƳA MACE



HIJABI MUTUNCIN ƳA MACE

tunda farko ma kamata yayi Ace munsan menene hijabin?

Hijabi kalma ce Allah Ta'ala yayi amfani da ita acikin Alƙul'ani inda yake cewa dangane da Matan Annabi "in zaku tambayesu wani abu to ku tambayesu bayan hijabi" wato hijabi yana zama labule (shamaki) wanda ya shiga tsakanin wani da wani, kamar ita mace da namiji ko kuma wanda yake na waje, muna iya cewa dai ba'a ganinka amma kana nan.

    /-/-/-/  shi hijabin yananu cewa bazai yiwu akanta ba sai dai yayi magana da ita bayan wannan shamaki wanda yana nufin in tana cikin ɗakinta kenan inda zata iya sakin jikinta ya zama ba za'a ganta ba, sai ayi magana da ita ta bayan shamakin,
Kuma ya kasance lokacin Manzon Allah (S) mutanen da kanje wajen matansa don tambayar su wani abu, sukan kasance suna ɗaki guda Amman basa ganinsu domin akwai wannan hijabin dake tsakanin su,

Ina faɗin asasin kalmar hijabin kenan, kuma sai ya zamana in zasu fita suna sanya tufafin da zai rufe jikinsu in banda fuska da tafin hannu da sutura wadda keda kauri, kuma be matse jiki ba, shima yau da gobe yasa ake kiransa hijabi ɗin, wancan Shine hijabi kenan, wannan kuma akwai "Jilbab da Himar" wanda duka sunayensu sun zo a Alƙul'ani, inda Allah Ta'ala yake cewa "Kace Da Matanka Da Ƴaƴan Muminai su matso da Jilbabinsu" shi jalbabi kamar doguwar riga ne daya sauka,
Su sakko da zannuwansu akan ƙirazanmu, wanda ya nuna akwai jallabiyya doguwar riga data sauka har ƙasa,
Akwai kuma Himar wanda shi ya rufe kai ne ya sauka har ƙirji,
Waɗannan gaba ɗayan su hikimarsu Shine kare gani tsakanin wani da wani abun, sai ya zama sunansu hijabi, mai-makon muce Jilbabi da Khimar,
Kamar yadda muka sani shi hijabi ya shiga tsakanin ganin namiji ne ga Al'aurar mace.

Allah bisa hikimar sa yayi mutane maza da mata, kuma yayi musu halitta daban daban, ya halicci mace ya sanya tanada jiki na jawo hankalin namiji wanda shi Allah ya sanya masa sha'awa, kuma yayi wannan ne da manufar dan asamu dangantaka tsakanin mata da miji, har ya zama akwai soyayya da sha'awa, har zamana akwai saduwa da haihuwa, to wannan ya halatta ne a tsakanin mata da miji, yana iya ganin tsiraicinta wanda zai bashi sha'awa, amma ba halatta ga kowa ba, ga muharrami kuwa wanda yake Ɗan Uwa ne ga mace akwai inda zai iya gani wanda bazai jawo hankalinsa ba gareta, ta kowane hali tunda ba za'a sauwala ko zai aureta bane, to wannan bazai haramta gareshi ba, kamar abinda ya bayyana na kafadu da kafafu, kamar dai yadda mata sukanyi shiga na yau da kullum a gida su saki jikinsu, shi wanda yake muharrami ne ya haramta ya aure ta, to shi zai iya ganinta haka.

Wanda kuma yake ba miji ba, ba muharrami ba to shine ajanabi, to shi kuma bazai ga komai haka ba sai fuska da tagukan hannu sai adon da ka iya bayyana a waɗannan wurare kamar zobe, tunda ya shiga abinda ka iya bayyana da kuma barima wanda akansa a hanci shima ya zama "Nazahar Minha" Tunda ba bazasu bayyana adonsu ba sai inda ya bayyana, kamar zobe ta fito a inda ya bayyana ko kuma barima na hanci  ko kunshi, wannan shine hijabi kuma hikimar sa kenan sai ya zama idan mace za'a kalle ta, to za'a kalle ta ne a matsayin mutum ba abin sha'awa ba.
"" 
Saɓanin à Wannan Zamain
Awannan nizamin an riga an ƙwace mutuncin mace daga gareta an mayar da ita abar sha'awa wato in ana so a jawo hankali ko wajen sayar da waɗansu abubuwa sai kaga an sata tsirara tsirara kusa da abin, sai tallata shi, ita kuma kullum anata tallata ta a matsayin aganta aji sha'awarta, ko akan titi ko anko ana wani annashuwa, ko wani biki sai kaga an bayyana ta, ko kai rawa ko tayi wani abu aji dadi, wannan haramun ne sai tsakanin ma'aurata biyu ma'ana mata da miji, wannan duka abinda taga dama tana iya yi mashi,
Koda kuwa rawa ne don ya halatta a tsakanin su, amma ga wani dabam haramun ne, to sai ya zamana abinda zai shamakance wannan shine asa abinda zai jawo hankalin namiji zuwa gareta, sai ya ganta amatsayin mutum ba abar sha'awa ba, wanann shine hikimar sanya hijabi.
Rubutawa Sakina Ahmad Kazaure 
Typing.. Ishaq Muh'd Suleiman

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post