GWAMNATIN BUHARI TA NEMI KASHE SAYYID ZAKZAKY(H) NE SABIDA TA SAMU CIKAKKIYAR DAMAN KASHE MUTANE A AREWA MASO GABAS, DA ZAMFARA DA SAURAN JIHOHIN KASARNAN, GA HUJJATA NAN👇



🇳🇬 Ma'asumah Hausa Nigerian News Updates. Tare da Wakilinmu Muhammad Aliyu Daud (Dansudan) Azare 070-32803940
  
Da Gwamnatin Buhari ta shirya kashe mutane a Arewa maso gabas da Zamfara da sauran jihohin Kasarnan, bisa umarnin Amirka da Isra'ila don su sace albarkatun kasar sukai qasarsu. Sai ta fara da neman ganin bayan Sayyid Zakzaky(H). Sabida kada ya taka musu birki ta hanyar bada kariya ga Al'ummah in suka zo yin wannan aikin ta'addancin nasu, sun san cewa yana bada kariya ga Al'ummah a duk lokacin da wani rikici ya tashi. Abu na kusa da ya faru kafin su kai masa hari shine, turowa mutane da suka yi da bom a hanyar tattaki, wanda aka kama daya da bom din a jikinsa, daya kuma kafin a kai ga kamashi ya tada nasa.Wannan kama mutum dayan ba qaramin tada musu hankali ya yi ba, haka kuma wanda aka kama shima bayan an tatsi bayanai a wajensa yanda ya falsa makircin Gwamnati yanda take kama su bisa dole da kuma gusar musu da hankali su turuso cikin mutane da bom. 

Sakinsa da kuma bashi kariya da aka yi, kamar yadda ya nema shi ya qara tunzura gwamnati ganin cewa ta kawar da Sayyid a doron qasa don ta samu ishashshen damar kashe mutane a Arewa maso gabas da Zamfara da sauran jihohin kasarnan.
Shine ta farmasa ta kashe mutane sama da dubu, don son ganin bayan ransa.
Wanda suka turo Sojoji da Kakinsu suka yi wannan aikin, sun san mu baza su iya canza kama ba suzo da wani suna na daban ba. Kamar yanda suke zuwa da suna na daban su kashe mutanen gari, mu in suka yi mana haka kamasu za muyi mu tona musu asirin da suke boyewa, cewa su suke kashe Al'ummah, aka kama mai bom a jiki bare mai bindiga!?.

  Tabbas sune suke kashe mutane a qasarnan da wasu sunannaki na qarya, inba haka ba su tsayar da kisan mana, amman a kullum qara qaruwa yake, sune suke yi ba kowa ba.
Wasu gawawwaki da mahara suka kashe a jihar Katsina kwanaki uku da suka wuce.

Hakama kashe mutane sama da dubu da suka yi da kuma cigaba da kashe mutane da suka yi a lokuta ma banbanta a fadin jihohin kasarnan ciki harda kafital Siti Abuja, haka kawai in an fito Muzaharar lumana ko kuma wani Taro. Wannan shi zai nunama cewa sune suke kashe mutane a qasar ba kowa ba, kawai riga suka canzawa,  in suka so su kashe mu sai suzo da kaki su kashe mu, sabida mu ba su isa su wawintar damu ba cewa wai wasu ne suke kashe mu, in kuma sauran jama'ar gari ne sai su cire kaki suje haka da wani suna na qarya.

Inba haka ba miyasa suka gagara tsayar da kisan da ake a qasar, amsa shine sune suke yin kisan.

Ku amsawa kiran Sayyid Zakzaky(H) da yake kira ayi adalci a dena zalunci, ku samu damar yin addininku 'yanda kuka fahimta ku rayu cikin aminci, ba yana Kira kuyi Shi'a ba ne,  a'a kuzo mu taru mu ture zalunci, lokaci ya yi mu amsa masa Mafita tana hannunsa.  Ya ku Al'ummah.
*FREE ZAKZAKY(H) WA UMMUNA ZEENAT*

*DANSUDAN AZARE 070-32803940*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post