DAGA:M.N.N UPDATES
TARE DA Asiya A Abdussalam
Watan Ramadan wata ne me albarka shine shugaban watannin Allah. Darajarsa da falalarsa ta nunnunka ta kowane wata ba tare da iyakancewa ba. Ramadan! Wata ne da rahama ke zubowa a cikin sa tamkar yayyafin ruwan sama. Jinkan Allah da ludufin sa na mamaye bayi. Allah na azurta talakawa da mabukata a cikinsa. Yana gafartama masu laifuka. Yana yanta yan wuta zuwa aljanna yana amsar addu'o'in mabukata ya cika burin masu roko. Allah buwayi gagara misali yana baje kolin ni'imarsa da baiwar sa ga bayi.Kuma yana dabaibayi ga ayyukan shedanci a cikin watan shedanu da iblisai suna kunyata a cikin watan ramadan.
Sannan kulle kulle, makirci da mugun nufi basu cin nasara a wannan wata saboda rahamar Allah da ke cikin sa
ALLAH KA SA MU DACE ALFARMAR WATAN RAMADAN.
Tags:
Tunatarwa