Filin Cuta da Magani
Daga: MA'ASUMAH NIG NEWS UPDATES
Tareda: Jibril Usman Sarki( 08149953832)
Kamar yanda sunan yake a sama, in muka ce _Dosage_ ana nufin ka'idar shan magani.Shi magani in aka bada shi sama da yanda maganin yake to matsala xata auku.sannan in aka bada k'asa da yanda akace nan ma akwai illa. Amman wannan illar tafi tasiri ga yara sbd su garkuwar jikinsu bata da karfi. Shi yasa aka tsara masu magani na ruwa daga randa aka haifesu zuwa shekara sha biyu. Daga sha biyu doka ta yadda a fara basu na kwaya.
Maganin ruwa duk murfi daya yana dauke da gram *125mg* wanda akan bawa yaro 1yr to 7yrs, murfi daya sama da haka 1 da rabi in yakai goma zuwa sama murfi biyu. Shine dede kuma ba xai illata antarsa ba. Amman a sani in yaro na zazzabi tofa ba zaka jika masa _pracetamol tab_ ba wannan ya saba doka sannan irinsu, _caps amoxyl, caps ampclox, cap tetracycline, tab panadol extra,tab ciproflaxacine_ ,dukansu karfinsu 500mg tamkar ka bawa yaro murfi hudu ne na magani na ruwa.ko ba likita bane kai kasan da matsla.
Haka ba zaka bawa yaro _iburofen tab, ceptrin tab, ofloxacine, cimetadine tab_dukansu 400mg ne kwatan kwacin ka bawa yaro murfi uku ne na mganin ruwa.
Sannan ba zaka bawa yaro _tab iburofen 200mg, tab cimetadine, tab metronidazole,_dss tamkar ka bawa yaro kusan murfi biyu ne babu kadan. Kaga overdose kenan wanda ke kashe yara.
In iyaye xasu lura in suna basu maganin kwaya xaka ga cikin yaro rititi ya kumbura irin kumbirin da masu ciwon anta keyi. Kuma ba kome bane antar yaron ne ke neman tabuwa.wasu yaram ma har idon su zai nuna kagansa yalo haka se ace shawara kuma duk antar ce ta fara tabuwa.jikin yaro na kumbura ya canza harshensa yai fari, alamun jinins ya kone ana aunawa zakaga befi 15℅ ba dole se an masa karin jini. Wani yaron zaka gansa ba kwari kuma duk illar maganin ne na kwaya.
Wani maganin kamar limotin tab, na tseda gudawa in aka basu zakaga gudawar ta koma atini kaga ya illata yaro kenan.
_Mafita anan shine_
Iyaye kome rashin babunsu ko temako su nema in yaro bashi da lfy ya kama kuma se sun bashi mgn a gida to a daure a siya masa na ruwa kamun aje asibiti.
Tags:
Cuta da Magani