DALILIN DA YASA MUKE YIN MUZAHARAR QUDUS

MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE


Alkalamin Ishaq Muh'd Suleiman

Da farko muna muzaharar Qudus ne bisa bin Umarnin Manzon Allah (S) domin kuwa shine ya sunnahnta mana damuwa da al'amarin Ƴan Uwanmu Musulmi Aduk inda suke,
Wani hadisi Manzon Rahama (S) yana cewa baya daga cikin mu wanda be damu da Al'amarin Musulmi ba,
Kenan dole ka damu da damuwar Ƴan Uwanka Aduk faɗin duniya walau farin cikinsu ko baƙin cikinsu,
Wannan ne yasa Imam Khomain (QS) ya assasa mana wannan muzaharar ta Qudus wacce ake gabatarwa juma'ar ƙarshen kowanne Ramadhan domin taya Ƴan Uwanmu Raunana Musulmin Palestine da aketa kashe su bisa zalunci sama da shekaru 60 kullum se ƙara zaluntar su ake musamman idan watan Azumi yazo Yahudawa na zafafa kai musu hare-hare ana kashe mata yara da tsofaffi dama matasa aikin kenan.


An ƙwace musu muhalli an maida su kamar kiyashi ana kashe su ba ƙaƙƙautawa kullum cikin ikon Allah se aka samu juyin musulunci na ƙasar irin ta hannun Ayatullahi Imam Khomain se yace dole mutashi mu tayasu ƙwatar Ƴancin su a saboda haka juma'ar ƙarshen kowanne watan Azumi se zama ranar jajanta musu ta hanyar yin Muzahara domin su.

Mu anan Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El Zakzaky (H) ne ya fara ɗabbaƙa wannan kira na Imam Khomeini Shine Mutum na farko daga nahiyar Afirika daya fara yin Muzaharar Qudus yanzu gashi kusan duk Afirika ana yinta a Jumu'ar ƙarshen Kowanne Ramadhan,
A Nigeria kaɗai ana yin Muzaharar Qudus a sama da birane 20 duk domin nuna damuwa da taya jaje ga Al'ummar Palestine da aketa gallazawa tsawon shekaru babu me magana akan zaluncin da ake musu Majalisar ɗinkin duniya (UN) sunyi shiru saboda America nada hannu dumu-dumu cikin wannan Baƙin zalunci da ake Musa,.

Wani abu da zai ƙara sawa mu nuna damuwar mu da kishi akan Al'amarin Palestine Shine Masallaci na uku mafi daraja da Yahudawa suka ƙwace wato (Masjidus Aqsa) Masallacin Qudus suka maida shi wajen saɓawa Allah da Izgili dashi, wanda kuma dole musulmi namiji da mace dole muyi iya iyawar mu wajen kare martabar wannan Masallaci me Alfarma na uku mafi daraja inda ta wannan Masallacin ne aka bi da Manzon Rahama (S) zuwa Mi'iraji amma yanzu Yahudawa sun ƙwace iko dashi sun mayar dashi wajen saɓawa Allah da sheƙar da jinin Musulmi,
"" ""
Abin takaici da baƙin ciki akan wannan al'amari na Palestine Shine yadda duniyar musulmi mabiya Sunnah sukayi likimo (shiru) aka lamarin duk da Al'ummar musulmin Palestine suma Sunnah ne, amma kuma hatta idan wani yayi basa so bayan su basuyi ba, Alhali suna sane sarai cewa Manzon Allah (S) yace Imanin Ɗayanku bazai cika ba har se yaso wa ɗan uwansa abinda yake so,
Amma na rasa abinda yasa Shi'a kawai suke shelantawa duniya tsananin zaluncin da akewa Raunanan Musulmin Palestine mabiya Sunnah, kuma Ƴan Uwansu à aƙida suna jin haushi meya dalilin hakan basa so atausaya musu ne ko basu san Sunnahr Annabi ne nuna damuwa da damuwar Al'ummar Musulmai dole ne ba? 
"
Ya Allah ka gaggauta kawo ƙarshen zaluncin azzalumai a Palestine dama duniya baki daya.

Ishaq Muh'd Suleiman

29/05/2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post