Kuyi shere Domin Wasu sugani Su amfana
Ma'asumah Nigerian News Updates
__
Manzon ALLAH (s.a.w) wata rana ya shiga gidan imam ALI A.S yana murmushi.
Sai yace: na zo gunka dan in maka bushara ya dan uwana, lallai jibril a.s ya zo min dazun da wani SAQO daga gun ALLAH, itace ALLAH ta'ala yace: ya AHMAD yiwa ALI bushara akan lallai masoyanka (imam ali a.s)......suna cikin 'yan aljannah, sai imam ali yayi sujjadah dan godiya ga ALLAH.
Sai imam yace: ya Ubangiji na kayi sheda kan cewa na basu rabin aikin ladan da nayi.
Sai sayyidah zahra a.s tace: ya ubangiji na nima kayi sheda na basu rabin aikin da nayi kyakkyawa.
Sai imam hassan da imam hussain a.s suka ce: muma mun basu rabin ayyukanmu kyawawa.
Sai shugaba manzon ALLAH S.A.W yace: ba fina kuka yi karamci ba, ni na basu dukkan kyawawan aiki na.
Sai mala'ika jibril ya sauka yace: ya manzon ALLAH S.A.W lallai ALLAH tabaraka wa ta'ala ya ce: dukkanku baku fini KARAMCI ba (ALLAH kenan), domin na yafe zunuban masoya ALI A.S kuma zan azurtasu da aljannah da ni'imarta.
Niko nace: TO AI BARKANMU 'YAN SHI'AR AHLI MUHAMMAD.
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ÀLI MUHAMMAD.
Dan sonmu ga MUHAMMAD DA IYALANSA ku yada dan ko wani dan shi'ah ya isa gare sa.
_Nakaltowa Mas'udu Dan Masani Shinkafi