BA ADDINI BANE YIN AZUMI A HALIN TAFIYA!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED 


Wasu mutane sun dauki addini ra'ayi ne, abinda mutum ya ga
dama ko yaso a ransa shi zai aikata, kuma yayi qoqarin
gamsar da mutane cewa abinda yake yi daidai ne.

Muna yin magana ne game da masu yin azumi a halin tafiyar
da aka qudurce ta ko aka fare ta kafin rana tayi zawwali.

Lalle ba addini bane, kuma ba aikin alheri bane yin azumi a
halin tafiya. Za mu kafa hujjarmu daga cikin manyan littafan
Sunnah kamar haka;
Bukhari ya riwaito da Isnadi zuwa kan Jabir Bn Abdullahi (R.A)
yace, Manzon Allah (S.A W W) ya kasance cikin wata tafiya, sai
ya ga wata inuwa wani mutum ya shigeta, sai yace;
" MENENE WANNAN ?"
Sai aka ce, " Me azumi ne !" Sai yace;
" AI BA ADDINI BANE YIN AZUMI A HALIN TAFIYA !"
-Bukhari, hadisi me lamba 1946
-Muslim, Sh:92, hadisi me lamba 1115.
To, a matsayinka na me da'awar Sunnah, me yasa za kayi
abinda ba addini ba cikin muslimci?
Tare da wakilinmu Ado Isah Guda

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post