Ku Danna photon Domin karantawa, Kuyi shere Domin Wasu su amfana
Ni Barr Rukayyat a hannun hagu Asiya a tsakiya sai Khadeejart Hamza a lokacin da CIO FOUNDER na Ma'asumah yakaimana ziyara a malunfashi |
__MECE CE SHI'A??
Kalmar shi'a aluga tana nufin mabiya ko mataimaka ko majibinta al'amuran juna.
Wannan kalma ta shi'a anfiyin amfani da ita akan gungun mabiya IMAM ALI (a.s)da iyalan gidansa tsarkaka.
Alkur'ani mai girma yayi amfani da wannan kalma ta shi'a ama'anarta ta luga.
Kuma ALLAH ta,ala yana cewa haqiqa daga cikin shi'arsa akwai "IBRAHEEM" acikin suratu (saffat 83) awani guri kuma dayake magana akan "ANNABI MUSA" (as) yace wannan yana daga cikin shi'arsa wannan kuma yana daga cikin maqiyansa SURATU QASAS AYATA 15.
Atakaice kalmar shi'a aluga ma'anarta shine gungun mabiya ko magoya baya dan haka in ance yan shi'a ana nufin masu goyonn bayan wani ko masu biyayya gawani mutum Amma a Isdilahi kalmar shi'a tana nufin mabiya IMAM ALI (as) da ahlul-bait(as)ne kai tsaye
kenan inmun saukaka bayani zamu iya cewa kenan shi'anci shine yarda da biyayya ga karantarwa dakoyarwa ta tsarkakan halifofin manzon Allah (s) guda 12 na Ahlul-bait(as) daga kan IMAM ALI(as) har zuwa Imam Mahadi [ajtf].
Zamu cigaba Insha Allah.
Daga Barr Rukayyat Muhammad Sulaiman.
Ma'asuma Nigerian News Update.