Rohoto.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates, Tare da -Idishia Jos.
Da safiyan yau Talata Dubbun nan Almajiran Sheikh Zakzaky (H) ne suka fito Zanga-Zangan lumana na kiran Gwannatin Nigeriya data gaggauta sakin Jagoran Barkan Musulunci Sheikh Zakzaky da matarsa domin a kai su Asibiti don kula da lafiyansu. Muzaharar dai Lumanan an fara ne a Federal Secretariat tsakiyan birnin tarayya Abuja.
Bayan an zaga ya ta bayan filin Eagle Square sai aka miko zuwa hanyar kofar majalisa ta kasa. Iso wan Almajiran Sheikh Zakzaky ke da wuya suka tarar da Jami'an tsaro a wajen sun katange wajen, inda anan aka mika musu takardan koke akan cigaba da tsare jagoran namu. Bayan anyi doguwar bayani gamsasshe ga jama'an tsaro dalilin zuwan mu, inda aka yi kuma kira garesu akan danne hakkin mutane BA tare da Hujja ba.
Tun dai bayan ta'addancin da sojojin NIGERIYA suka yi na kisan 'ya'yan Sheikh Zakzaky da harbin sama da 1000+ daga cikinsa Almajiran Sheikh Zakzaky ake tsare dashi a Abuja. Sama da shekara daya ana gudanar da wannan muzaharori na lumana a garin Abuja kullum da kullum. Ansha kai koke jamalisar Tarayya da Ofishin kare hakkin Bil'adama amma har yanzu babu wani mataki da aka dauka don fita da Sheikh Zakzaky kasar waje kamar yadda Kotu ta bada Umarni.
A kwanakin baya kadan likotici suka zo duba lafiyansa amma suka ce ba zai yuwu a mai magani anan ba sai dai a fita dashi waje amma har yanzu Gwamnati tayi Burus da wannan magana shiyasa muke fitowa don mu jadda kira lallai a gaggauta sakin Sheikh Zakzaky domin duba lafiya sa tare da mai dakinsa. Anyi lafiya kuma an tashi lafiya.
Tags:
Labaran Duniya