Yi shere Domin Wasu su amfana
Ma'asumah Nigerian News Update
Daga Wakiliyar mu Sakina Ahmad Kazaure
Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yana fuskantar ƙalubale daga Azzalumar gwabnatin zamaninsa da kuma Malaman zamaninsa kwaɗayayyu,
Duba da yanayin da muke ciki zan so mana karin haske daga kowanne ɓangare da Sheikh yake fuskantar ƙalubale daga garesu,
ƘALUBALE DAGA HUKUMOMI
waki'o'in da suke afkuwa a gwagwarmayar Sheikh (H) waɗanda ke tattare da kisa, kamu, tsarewa, da ɗauri, à gidajen kurkuku da kuma Sauran nau'in wahalhalu da dama ga Sayyid (H) akaran kansa da Sauran Ƴan Uwa dama harkar baki ɗayanta waɗansu abubuwa ne da suke a matsayin ƙalubale kai tsaye daga hukumomi Sayyid Zakzaky ne yake fuskantar wannan ƙalubale dama ita harkar kanta,
Sayyid Zakzaky ya jima yana fuskantar wannan ƙalubale daga hukumomi tun farkon fara wannan da'awarsa,
Kasantuwar hukumomi suna ganin kamar ta hanyar afkar da waki'o'in to zasu tsayarwa ko kuma aƙalla su kawo cikas a tafiyar gwagwarmaya a lokutan da suka ga dama, amma kuma da Ikon Allah sai lamarin ya kasance duk lokacin da suka afkar da waki'a to ƙarshe abin yana komawa ne kansu, kuma ya zama taimako ga harka Islamiyya, amma kuma hukumomi basa daddara sai cigaba da afkar da waki'a sukeyi a yankuna daban-daban na harkar Musulunci, da yake lamarin baya zama darasi garesu, Sam basa ɗaukar darasi, sukan turo Ƴan sanda suzo suna kama Ƴan Uwa, akan kuma turo Ƴan tayar da tarzoma waɗanda kan zo suna buɗewa yan uwa wuta suna harbinsu da harsasai masu rai,
Akwai kuma Ƴan tauri, Ƴan banga, Ƴan daba, da Sauran wasu Ƴan iskan gari, waɗanda su kuma daga baya bayan nan hukumomi suka fara amfani dasu wajen afkawa Ƴan Uwa ma'abota harkar musulunci a birane, garuruwa, ƙauyuka da dama Sauran wurare.
Sheikh Zakzaky yasha kamu da dauri a hannun hukumomin ƙasarsa Nigeria ansha kamashi da azabtar dashi da daure shi a lokuta daban-daban ya zuwa yanzu hukumomin Nijeriya sun kama Sheikh Zakzaky har sau goma (10) kuma jimlar shekarun da yayi a tsare sun doshi shekaru 17 ya zauna a gidajen kurkuku na jihohin nigeria daban daban daga ciki ya zauna kurkukun Zaria, Kaduna, Sakkwato, fatakwal, Lagos, da Abuja, cikin wuraren da aka taɓa tsare shi hadda wurin azabtarwa da bincike daga ciki akwai inda ake kira (interrogations center) a Lagos da kuma wuraren tsaro na musamman na jami'an leken asirin DSS a Abuja,
Bisa abinda yake tabbatacce azahiri Shine daga lokacin da Sheikh Zakzaky ya fara da'awarsa a shekarar 1980 zuwa yanzu mafi yawan gwamnatotin nigeria sun ɗaure shi a gidan yari wasu gwamnatocin ma sun daure shi fiye da sau ɗaya, yayin da wasu gwabnatocin ke cigaba da ɗaure shi yanzun haka.
Gwabnatin soja ta janar olusegun Obasanjo ta tsareshi à shekarar 1979 a Zaria ta kuma sake kamashi a Sokoto ta tsareshi a farkon shekarar 1981.
Gwabnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari ta kama Sheikh Zakzaky ta ɗaureshi tun daga wajen tsakiyar shekarar 1981 zuwa 1984.
Gwabnatin soja ta janar Buhari ta daure Sheikh Zakzaky a wajajen karshen 1984.
Gwabnatin mulkin soja ta janaral Ibrahim Babangida ta tsare Sheikh Zakzaky a shekarar 1987 - 1989 sannan Har wala yau gwamnatin janar Ibrahim Babangida ta sake kamawa da Sheikh Zakzaky a shekarar 1992.
Gwamnatin mulkin kama karya ta janar Sani Abacha ta daure Sheikh Zakzaky a shekarar 1996 ƙarshen shekarar 1998.
Gwabnatin mulkin danniyar farar hula ta Muhammadu Buhari ta kama Sheikh Zakzaky ta tsare a ƙarshen shekarar 2015 wanda har zuwa yanzu a farkon shekarar 2019 ba'a sake shi ba.
Bisa wannan lissafin, zamuga cewa gwabnatocin soja ne suka fi yawan kamawa da tsare Sheikh Zakzaky (H) awuraren tsarewa akalla goma sha bakwai, daga cikin tsarewar da aka masa an taba tsareshi a DUNGEON wani gurin tsarewa na ƙarƙaahin ƙasa, wanda mutum baya iya banbance dare da rana,
A wata hira da akayi da Sheikh Zakzaky Yace :- an tsareshi a wani wuri wanda yake shi wannan wurin ba akan gane dare da rana bane, amma wani lokacin akan fito damu (dan suna yarda mutum yayi wanka sau ɗaya a mako) sai a fito da mutane wajen suzo duk a wuri daya asa musu botikai (su tuɓe suyi wanka) sai suka ni ban fito ba saboda sunayin tsirara ne har wani yace mun kai baza kayi wankan bane? Sai nayi masa shiru sai yace auho, dan kai Musulmi ne ko? Sai ya yarda ni na dinga yin wanka na ni kaɗai.
To saboda tsabar tsarewa da akayiwa Sheikh Zakzaky an haifi Ƴaƴa uku daga cikin Ƴaƴansa ne a lokacin yana tsare ne a gidajen kurkuku misali an haifi ɗansa na farko Sayyid Muhammad yana kurkukun ƙiriƙiri a Lagos, an haifi Sayyida Nusaiba yana kurkukun Kaduna.
Writing Sakina Ahmad Kazaure