ALKALAMI KA FI REZA KAIFI*

Kaye shere Domin Wasu sugani su amfana

M. I. GAMAWA

*Nankarwa a jikin belbela (IV)*

Mun dawo daga hutun dolen da muka tafi. Mun yi hutun jaki. Ba hutu muka je ba. Mun harari Farfesan 'yan rudu, Umar Labdo ne. Mun dawo da yaddar Allah. Za mu ci gaba da mamakin yadda nankarwa ta bayyana a jikin belbela. 

Mun tsaya  a inda kabilar Ibo ke wa Hausawa kazafi kan wasu abubuwa da a lokacin mutanen Arewa Hausawa ba su san su ba. Mun fadi mafi karanta daga mai yawa a rubutun da ya gabata. Yanzu kafin mu yi linkaye a cikin tarihin masifar da yakin basasa ya janyo mana, bari mu yi kiwon gwanki, don bayyana yadda kabilu biyu manya da Bature ya hada su wuri guda da ’yan Arewa ko mu ce Bahaushe suke. 

Bari mu fara da Bayarbe. Yaya rayuwar Bayarbe take? Yaya yake mu'amala da Bayarbe dan’uwansa? Yaya yake mu'amala da wanda ba Bayarbe ba? Yaya halinsa yake in shi ne a karkashin wani? Yaya yake in shi ne a sama, wasu na karkashinsa? Shin yaya rayuwarsa take in yana zama a nesa da yankin da ya fito? 

Bishop Ajayi Crowder ya yi bayanin tarihin Yarabawa da halayensu a cikin littafinsa mai wahalar samu da ya sa wa suna THE ORIGION OF YORUBAS. Bishop Ajayi ya yi tsokaci kan halayen Bayarbe guda biyu masu tsananin muhimmanci. 

Kamata ya yi duk wanda zai yi mu'amala da Bayarbe ya san wadannan halaye, ko in ce ya san Bayarbe da su. Sune rashin yafiya da ramakon gayya da zarar damar hakan ta samu. Rashin yardar Bayarbe da kowa bai ma kai abin da Ajayi zai bata lokacinsa wajen magana a kai ba. Kowa ya san Bayarbe kan haka. Za mu yagi abin yaga daga halin Bayarbe bisa la'akari da zamantakewar Najeriya da mutanenta a daya hannu. 

Za mu bi wadannan halaye da Bishop Ajayi ya ambata daya bayan daya. Amma dole mu fara magana a kan rashin yarda irin ta Bayarbe. Na farko shi Bayarbe bai aminta da kowane mahluki ba. Bayarbe dan’uwansa ko wata kabila. Sai dai akwai magana a nan. Za mu zo kanta daga baya. 

Rashin yarda a tsakanin su shi ne abin magana da farko. Kamar yadda masu ba da tarihin Yarbawa ke badawa. Wasu sun ce Bayarbe na farko a doron kasa shi ne Oduduwa. Wasu sun ce Oduduwa ya sauko daga sama bayan ruwan dufanan zamanin Annabi Nuhu (as). Wasu kuma sun ce da yake ga Lamarudun Babila. Wasu kuma sun ce daga Hijaz, wato inda ake ce wa Saudi Arebiya ya zo. Sai dai masu tarihi sun yi ittifaki cewa Oduduwa ya sauka a ILE IFE ne. Za mu ci gaba insha Allah. 

*GWARAWA SUN TSARE WA OSINBANJO HANYA*

Ba ma zaton mai karanta ALMIZAN zai jahilci Osibanjo. Sai dai babu mamaki a ga laya a aljihun dan Izala. Ga wanda bai san shi ba. Shi ne Mataimakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari. 

A tsarin Dimokradiyya shi ne na biyu a mukami a duk fadin Najeriya. Da yanzu Buhari zai tad da Kakanninsa, tabbas Osinbajo ne zai zama Shugaban kasa. An ki, ko an so. Haka dokokin da ke tafiyar da kasar nan suka tanada.

An yi haka sau uku a kasar nan. Daya lokacin da aka kashe Murtala Ramat Muhammad. Inda aka nada Mataimakinsa Obasanjo, ba tare da bata lokaci ba. Haka lokacin Umaru Musa ’Yar'aduwa. Shi ma da ya riga mu gidan gaskiya, sai mulki ya koma hannun Jonathan. Abacha ya bar duniya ba shi da Mataimaki tsayayye. Haka ta faru bayan kama Mataimakinsa Laftanar-Janaral Oladifo Diya. Amma duk da haka, na uku a girman mukami ne ya gaje shi, wato Janar Abdussalami Alhaji Abubakar. 

Akwai kwanakin da doka ta kayyade wa Shugaban kasa zama a kasashen ketare. In ko ya wuce su, dole ya mika mulki ga Mataimakinsa. Wato ga dukkan alamu mataki daya ne kawai ya rage wa Osinbajo zama Shugaban kasa. 

A satin da ya gabaci wanda ya gabata, Gwarawa 'yan kasa, masu tinkaho da cewa Abuja garinsu ne, sun yi zanga-zanga a kan titin da ke zuwa filin jirgin saman Abuja. Hanyar kuwa ita ce daya tilo mai kai mutum filin jirgi daga Garki, Abuja. Gwarawa, suka tare hanya har ta kai sun hana duk wanda zai wuce don tafiya filin jirgin saman Abuja mai suna Nnamdi Azikiwe wucewa, komai saurin mutum, kuma ko shi waye, dole ya tsaya. 

Ana cikin haka, sai ga Mataimakin Shugaban kasa, Yomi Osinbajo ya kunno kai da tawagarsa zai wuce zuwa filin jirgi. Gwarawa suka tsai da shi da tawagarsa, suka hana shi motsawa. Ganin abin da ke faruwa, nan take Osinbajo ya sauko daga motarsa ya fara bai wa Gwarawa hakuri. Wasu na ihu, suna “ba mu yarda ba!” Wasu na cewa, “karya ne!” Da haka har ya ciwo kansu, suka bude masa hanya ya wuce. 

Masha Allah. Osinbanjo ya san munin taba Gwarawa. Ya san abin da doka ta tanada wa wadanda suka tsare wa wani hanya, komai girman mutumin. Ya san cewa, in da ya sa an kashe wani, tabbas ko da ba a yi masa komai a wannan duniyar ba, tabbas akwai hisabi a lahira. Yanzu babu ran Bagware daya da Osinbajo zai biya gobe kiyama da sunan an tare masa hanya. Shi a wa da zai zubar da jinin dan Adam don kawai an tare masa hanya? Don yana Mataimakin Shugaban Najeriya? 

Sau nawa cunkoson motoci ke tsare masa hanya a Legas? Sau nawa cunkoson mutane ke tsare masa hanya a kasuwa a duk tsawon shekarunsa? Sau nawa shanu ko wasu nau'i na dabbobi ke tsare masa hanya a tsakanin Legas da garinsu? Sau nawa yake fama da tsare hanya daga direbobin tirela a duk lokacin da aka munana musu? Dadin dadawa sau nawa mutanen Cocinsa ke tsarewa mutane hanya? Sa'annan shekaru nawa zai yi yana kan mulki? Tabbas shekaru takwas, in komai ya tafi daidai. Wannan shi ne tunanin da Osinbajo ya yi a yayin da Gwarawa suka tsare masa hanya a hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Abuja. Madallah da haka. Daga ranar zuwa yau babu Bagwaren dazai tuhumi jinin dansa ko matarsa. Ba Bagwariyar da za ta tuhume shi jinin mijinta. Karatu da aiki da shi ya yi tasiri a nan. 

Wani abin dubawa a nan shi ne Osinbanjo dai Bayarbe ne, mutumin kudancin kasar nan. Abin na iya zama masa jarumta da ya kashe 'yan Arewan da suka nemi muzanta shi a matsayinsa na Mataimakin Shugaban kasa. Amma ya daure, ya cije, ya ki kisa. 

Wani dalili na biyu da zai sa ya ci bulus, da ya sa an yi kisa shi ne karfin jaridun da yankinsa na Yarbawa ke da shi a kasar nan. Da abin ba zai gagari jaridun kudancin su ce an kai masa hari ne, masu kare lafiyarsa suka kubutar da shi, garin haka aka kashe wasu. 

A matsayinsa na Farfesa wajen sanin dokokin kasa, tabbas ya san abin da zai ce don fid da kansa, amma duk da haka ya mutumta rayukan ’yan’uwansa mutane. Ko da cewa ya yi, "Ni da Shugaban Sojojin Najeriya wane ne gaba?" Wannan tambayar kawai ta isa ta zama hujja ga wadanda za su tuhume shi. Ko da yasa an kashe su a inda suka tsare masa hanya, tabbas yana da karin hujja. Zai ce shi bai bi su gidan Sarkin Gwarawa cikin dare ya kara kashe su ba. Bai je makabartunsu ya baje su kamar yadda Buratai ya yi wa ’yan Shi’a ba. Bai je ya rusa gidajensu da wajajen ibadarsu ba. Bai kona gawarwakinsu ba. Watakila ya ce bai kai wadanda aka raunata da harsasai kurkuku, maimakon asibiti ba. 

Mun gode Allah da Osinbajo bai zubar da jinin ’yan’uwanmu Gwarawa ba. Tabbas, dole a yaba masa da irin wannan ’yan’adamtakar da ya nuna. Kasancewarsa cikin gwamnatin mutanen da suka fi kama da dabbobi, bai mai da shi dabba ba. Zamansa a cikin gwamnatin shagalallun da suke zaton ci gaba da mulki har abada, bai ruda shi ba. Zamansa cikin mashaya jinni, bai mai da jini zuma ba gare shi. 

Zamansa cikin masu kisa ba kakkautawa bai mai da shi makashi ba. Zamansa cikin ’yan Arewa masu zubar da jinin ’yan’uwansu ’yan Najeriya bai mai da shi mai zubar da jini ba. Bai dauki shekaru takwas kacal a matsayin shekaru dari ko fiye da haka ba. 

Tabbas giyar mulki na bugarwa, har ta sa tambele, amma har yanzu ba ta yi wa Osinbajo kamun kazar kuku ba. Ina masu ambaton tatsuniyar da ta fi ta gizo da koki zama tatsuniya, masu cewa wai an tsare wa Shugaban Sojojin Buratai hanya?

In za a fadi matsayin mukamin Shugaban Sojojin a mulkin farar hula, sai mu ce ba wai yana kasa da Ministan tsaro ba ne kawai. Yana kasa ne da Fam-Sakatare. Ba shi da bambanci da Shugaban gandirebobi da na kwastom. Amma ya kashe sama da mutane dubu bisa karyar tsare masa hanya. 

Dan Arewa ke nan wanda bai san mutumcin rai ba. Shi dai ya kashe kawai. Bayan kisa sai Baba-na-kotalo da ke Abuja ya ba da halascin wannan mugun aiki. Da yake shi ma dan Arewa ne kamar karen nasa, Buratai. ’Yan kudanci da ’yan kasashen waje kuma suna kallon dabbobi masu kashe jama'arsu. 

Ba wai Osinbajo ya kayatar da duniya kawai ba ne, har ma ya kara wa addininsa kiristanci farin jini a wajen masu neman addinin. Don ba kowa ne ya san bambancin Musulunci da Musulmi ba. A wajen wanda bai san addini ba, Buhari da Musulunci, duk daya ne. Gare shi duk abin da Buhari ya yi yardajjen abu ne a wajen addininsa. Haka ma Osinbanjo. Da ma an dade ana yawo da bidiyon da ya nuna 'ya'yan musulmi suna sace kayan shahidanmu da Sojojin Muhammadu Buhari suka kashe a Gyallesun Zariya a cocunan duniya. Yanzu kuma an sake samun damar nuna wa duniya tausayi da mutumta rai, irin na kirista Osinbajo. Sabanin rashin imanin musulmi Buhari da talakawansa na Gyallesu da Malaman wahabiya ashararrun nasi.

Washegarin tsare wa Osinbajo hanya, sai ga Shugaban samarin da suka aikata aikin a gidan talabijin na AIT, cikin wani shirinsu mai farin jini da ake kira KAKAAKI. Bai yi kasa a gwuiwa ba ya nuna wa duniya cewa sune suka tsare wa Osinbajo hanya. Sai kaka? Hakkinsu suke nema. Anya wannan Gwarin bai fi duk Hausawan Najeriya sanin hakkinsa ba? Ina wayewar da Bahaushe ke fankama da ita a kan Gwarawa? Tabbas reshe ya juya da mujiya. Ko mu ce mai doki ya koma kuturi. Tir da Bahaushen yau! 

Babu wanda ya ce, a hukunta Gwarawan da suka tsare wa Osinbanjo da wasu dubban ’yan Najeriya hanya. Babu Malaman Musulmi ’yan duk inda ta fadi sha, balle Malaman Kirista masu dogon tunani da hangen nesa da suka ce a kama su, balle su ce a kashe su. Shin hukunci kisa don tsare hanya na dan Shi’a ne kawai?

Ina bakaken jahilai daga Musulmi masu cewa, "Yaya za a tsarewa Shugaban soja sukutum hanya" Ga shi an tsare wa Mataimakin Shugaban kasa hanya. Sai me?

Gaskiyar magana ita ce jinin wasu na da tsada, amma na Musulmi ya fi ganye a daji arha. Da fatan Musulmin duniya za su taimaka wa Musulmin Najeriya da addu'a ko Musulmin Najeriya za su dawo hankalinsu, su fahimci cewa jinainensu ba abin zubarwa ba ne haka siddan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post