Daga Kanwarku Sakina Ahmad Kazaure
Sayyida khadija ta kasance mahaifiya ga sayyidatul-nisail-alameen fatimatuz zahra (a.s)itace matar manzon Allah (s)ta farko kuma itace mahaifiya ga yayansa.
Sayyida khadija ta yi wafati aranar 10 ga Ramadan wafatin ta ya zama wani babban abin bakin ciki ga manzon Allah dama al'ummar musulmi.
Sayyida khadija ta kasance mai taimakon addini da dukiyarta don babu Wanda ko wacce ta sadaukar da dukiyar ta ga addinin nan a duk cikin sahabbai kamar sayyida khadija (a.s) saboda yawan sadaukarwar ta yasa manzon Allah yace:" Addinin nan ya kafu ne da dukiyar khadija da kuma takobin Ali (a.s).
Itace ta farkon imani wadda ta farayin imani da manzon Allah (s)kamar yadda hadisi yazo daga imam Ali (a.s) yana cewa:"munyi wata shida ba mai sallah a doron kasa sai manzon Allah da khadija alhali nine na uku su." Ta kasance ita ce matar manzon Allah (s) ta farko bai auri wata ba kafin ta kuma bai hada ta da wata ba,har tabar duniya wadda duk cikin matan manzon Allah (s) ba wadda ta samu wannan.
Bayan wafatin ta manzon Allah (s) ya kasance yana yawan ambaton ta da yabon ta Wanda har sai da girmamawar ta ta shafi kawayen ta kamar yadda bukhari da Muslim suka ruwaito cewa: uwar muminai Aisha tace:banyi kishin wata mace ba kamar yadda nayi kishin khadija alhali kuma ni ban risketa ba,kuma manzon Allah (s) ya kasance idan ya yanka akuya yana cewa: Ku aikata izuwa ga abokan khadija, sai na bashi haushi wata rana nace:khadija kuma? Sai manzon Allah (s) yace: lallai an azurtani da sonta. Kuma yadda manzon Allah (s) yake yawan ambaton ta da yabon ta na irin taimakon da ta bayar wurin tabbatuwat addinin musulunci. Wata rana manzon Allah (s) ya yabeta a gaban Aisha (R)sai tace: ya manzon Allah! Me yasane kullum kake ambaton wannan tsohuwar? Alhali Allah ya baka mafi alherin ta? (Tana nufin ita kenan) sai manzon Allah (s) yayi farat yace "Sam-sam wallahi Allah bai bani wadda tafi khadija ba.tayi imani alokacin da mutane suka karyatani ta kuma bani dukiyar ta alokacin da mutane suka hanani,kuma Allah ya azurtani da yaya daga gareta alokacin da ya hanani yaya daga wasu matan. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
Sayyida khadija ta kasance tun anan duniya Allah yayi mata albishir da gida na zinariya a aljannah kamar yadda Muslim ya ruwaito a sahih nasa haakim ya ruwaito a mustadrak nasa.yana cewa: manzon Allah (s) yace: jibril yazo mani sai yace: ya manzon Allah! Ga khadija nan tazo maka kuma a tare da ita akwai wani kwano Wanda cikinsa akwai miya ko abinci ko abin sha,idan tazo maka ka karanta sallama a gareta daga ubangijin ta kuma daga gareni sannan kayi mata albishir da gida na zinariya Wanda ba hayaniya a cikin sa kuma ba gajiya.
Sannan sayyida khadija ta kasance daya daga cikin mafifita matan duniya baki daya kamar yadda turmizi ya ruwaito daga anas cewa manzon Allah (s)yace: mafifita matan duniya sune:- Maryam bnt imran, khadija bnt khuwait Fatima bnt Muhammad da asiya bnt muzahim.
Ya isheka sanin matsayin sayyida khadija (a.s) idan kayi la'akari da cewa a duk duniya ba wacce ta zamo sila wurin yaduwar zuriyar manzon Allah (s) sai sayyida khadija (a.s) ta hanyar yar ta fatima.
Assalamu alaiki ya sayyida khadija.
*Tare da Wakiliyar mu sakina Ahmad kazaure*
Tags:
Munasabobi