Abunda yafaru Dani A Da'irar malumfashi...!!!!

Ni Mas'udu Dan masani Shinkafi tare da Abokin Aikina Mudansir Bara'a Malunfashi ayayi. Danakai masu ziyara a satinnan


Tun Ranar Assabar na taso daga Ogun State domin Kai wasu ziyarori da natanada domin Ganawa da wasu sahihan bayin Allah a Zariya da Malunfashi inda har kano naso na wuce Amma saboda ina Cikin yanayi na matsananciyar rashin lafiya bansamu damar hakan ba,,,,

Bayan saukata Zariya na Kira marubucin Dan uwannan Wakilin ma'asumah Auwal Adam sidi wayar bata shiga saboda rashin network a inda yake, domin tun ina a hanya yake faman Kirana yaji ina yanzu haka?? Wannan tambayar dayakeyi agareni kenan. ,,  bayan nata faman Kira bansamu ba fiye  dasau goma sai na tura masa sako (Text Message), watsam sai nasake Kiran waya zuwa ga Muhammad Sadis shima wakilinmu bayan shiga sai kuma yazamana yana Cikin makaranta, sanadin haka bamu samu Ganawa a Zariya ba , Inacikin wannan yanayi sai naji ana ambatar malunfashi mai sauri, a cikin Tashar Ply ober dake cikin Zariya , 

Nanufi wajen da sauri dama dagani sai Traveling Back dita sai naje nashiga bayan na biya kudin mota na cif Amma na tsorata da abunda na gani acikin motar.........mota ta lula damu har malunfashi, A inda inakan hanya naga kiran Auwal Adam sidi bayan yaga sakona nake bayyana masa nakama hanyar malunfashi, a gaskiya baiji dadiba nabashi hakuri kuna ina Dada bashi insha Allah anatare, tafiya direba yakeyi akan kwalta dake shinfide ga titin Har cikin garin Malunfashi.
 dama nayi waya da ABOKINA kuma DAN UWANA Mudansir Bara'a Malunfashi, sai gashi na riskeshi a inda ya sanar Dani akan Dan okada.

Bayan saukata a unguwar  naci karo da cincirodon Mutane bayin Allah mabukata Wasu tsofaffi guragu da makafi dss wasuma kawosu akeyi  daga kauyuka duka suntaru a kofar gidan da bazan iya kiyasta yawan mutanen ba, Duka sun taru a kofar gidan da dan uwa Mudansir din ya dosa domin ga alama cikin gidan zamu shiga Kai tsaye,.
Gida ne kirar zamani mai cike da kyawawan tsari sai dai ga alama ba kowa acikin gidan Illah yan uwane Almajiran Mlm Zakzaky (h)  daketa faman Aikace-Aikace na Banbare sabbin kwalaye taliya da makaroni a inda akesasu a leda daya tare da tsabar kudi a kowane kunshi naira 300 da ake baiwa mabukatan dana baro a kofar gidan sunyi Cincirindo, kowane mabukaci dauri daya da kuma tsabar kudin cefane 300, Saboda Allah (T) Ladar zuwa ga mahaifiyar wannan Dan uwan daya sadaukar din, A inda akesawa wannan cibiya bayar da wannan kyauta ZAINAB FAUNDATION, 

Naga tarba,
Naga karamci,
Naga yan uwantaka ta musulunci Wadda tafi ta jini,
Naga Mabiya  Manzon Allah Da iyalansa (s),
Naga Tarbiyyar da koyarwar Mlm Zakzaky (h),
Naga Ilimantarwar Mlm Yakub katsina
Tare da jinjinawa Wakilin yan Uwa mlm Kabir Imam.
Hakika naga yan shi'a ....

Bansan abunda zanfada ba saboda tsantsar kauna da shaukin da suka nunaman kamar su hadiyeni, da suna iya daukata suyi tawaina da zasuyi, Idan natuna Abunda mlm Mudansir Bara'a yayiman na hango Irin Tsabagiyar Dawainiyyar da Abokin Aikina a Social media kuma Dan uwana Mlm NASERR YA BABA MALUNFASHI 
yayiman sai na zubar da kwallah akai... 

Mlm Naseer yababa Malunfashi tare Dani da muadsir ayayin da muka ziyarci Rastoran domin cin abinci


Bazan manta da Dan Uwa Malamina MLM AHMAD MAI KUSA MALUNFASHI ba, gasu Dan Uwa Shafi'u Shaf-Shaf ga kuma Su Abdulganiyyu.... Da kuma dinbin yan uwan daban rike sunan suba, Uwa uba kuma Wakilan shafin nan Mata Na MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE, Mata Musamman Barr rukayat da nasamu dinbin kyaututuka a hannun ta bihakki fatimah ma'asumah, ina gdy.

Mizance da Asiya Abdussalam bisa da rashin kwanciyar hankalinta harsai dataji  na sauka gida lfy. Gasu Sayyadah kuma saliha Khadeejart Hamza ina gdy mai tarin yawa da Dukkan sauran yan Uwa ina shaukin ku duk dacewa banso baro kuba kuma bakuso hakanba, aman afuwa... 

Wakilanmu Mata barister rukayyat daga hagu sai Asiya Abdussalam a tsakiya sai khadeejart Hamza a wajen zaman da mukayi


Hakan tafaru ne saboda yanayi na rashin lafiya da nake fama da ita Amma Alhamd inakan samun lfy d yrdar Allah kuma na sauka gida lafiya ayau dinnan ngd

Illahy y saka muku da mafificin Alkhairy yabar Ladar zumunci yakara yalwar arziki, ya kuma gaggauta baiwa su mlm lafiya yadawo mana dasu acikinmu, ya Allah kasanya muzamo mataimaka wannan bawon Allah ba mabiyansa kadai ba bihakki fatimah wa abiha.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post