Inji -Sheikh Adamu Tsoho Jos.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates. Tare da -Idishia Jos.
Manzon Allah (S) yake cewa ku tuna da yunwan da zaku sha da kishin ruwan da zaku sha a wannan wata na Ramadan ku tuna da yunwan ranar kiyama da kishin ruwan ranar kiyama. Wato bima'a na azumin ka ya tunantar da kai ranar kiyama ya tunatar da kai tsayuwan Mahashar, Manzon Allah yace ku yawaita sadaka akan fakirai daga cikin ku da miskinan ku dake cikin ku, kada ya zamo kai kaci makocin ka fakiri shi ya kwana da yunwa. Manzon Allah (S) yaci gaba da cewa ku girmama manyan ku kuma kuji tausayin na kasa da ku, ku sadar da zumuncinku ku kiyaye harshen ku, ku runtse idon ku da ganin abinda bai halarta ku gani ba.
A watan Ramadan ba'a son mutum ya yawaita kalle-kalle in ba kallo na halal ba, kada ka bari ka kalli haram domin kallon haram kamar kibiyane in ya shiga zuciyarka yakan lalata zuciya din. Sannan ku kiyaye jin ku daga abinda bai kamata kuji ba, kada kuji maganar banza ko batsa, ko wake-wake na banza. Mun karanta ruwaya cewa a watan Ramadan dare da rana ba'a waka wakan ko koda ko na musulunci ne koda yabon Annabi ne to (Makaruhine) a watan Ramadan. A wani wata da bana ramadana ba to an karhantashi da ranar juma'a, da daren juma'a. Abinda ake so ka shagaltu dashi shine karatun Qur'ani zikiri, salatin Annabi, istigfari da sauransu.
Don haka ya zamo cewa ana so mutum ya kiyaye harshensa da jin sa, kaga nan hatta begen Manzon Allah (S) kaga abu ne mai kyau amma aka ce a watan Ramadan ya zamo ka ja baya da ji abinda ake so mutum ya yawaita yi shine karatun Qur'ani. Manzon Allah (S) yace; ku tausaya wa marayun mutane to kuma sai a fausaya muku, wannan wata na Ramadan wata ne da ake so a tausayawa marayu. Ya kamata ace a wannan wata na Ramadan musulmai su yawaita zuwa ziyara gidan Marayu muna sadar da musu alkhairi muna faranta musu rai ta hangar yi musu alkhairi da ciyar dasu da tufatar dasu da faranta musu rai wannan yana da matukan muhimmanci.
Manzon Allah (as) yake cewa; Ku tuba wa Allah da zunubanku a cikin wannan wata mai girma da daraja, ku daukaka hannayen ku, ku daga hannayen ku da addu'a a lokutan Sallah bima'ana idan kuna Sallah a watan Ramadan kuna yin alkunut ku yawaita Alkunut, harma tsawon Alkunut da za'ayi a sallah to yana girmama lada da daraja na shi mai Alkunut. Domin lokacin Sallah shine mafificin sa'a shi yasa addu'a ana son a lokacin sallah ka yawaita. A wannan lokaci da bawa ya tsaya yana Sallah to Allah yana kallon bayin sane kallo na rahma, kuna yazo cewa duk wanda Allah ya dubeshi kallo na rahma to ban zai taba azabtar dashi ba.
Allah (T) yana amsa wa bayinsa idan sun munajati dashi kuma yakan amsa musu idan sun kirashi, yakan bawa bayi idan sun kirashi, Yakan kuma karban addu'ansu idan sun kirashi. Manzon Allah (S) yace; Ya ku mutane ku sani fa ayyukan ku da zakuyi a wannan wata jinginenne ne da ayyukanku don haka ku fanshi rayukanku da yawaita istigfari a watan Ramadan. Lallai bayan ku yana dauke da nauyin zunubai mai yawa ku saukake nauyin zunubin ku da yawaita Sujuda, kayi sapoah kayi sujja shukur ku yawaita sujada akwai lada. Lallai Allah (T) ya rantse da buwayansa cewa ba zai azabtar da masu sallah ba da masu sujjada. Kuma ba zai razanar da masu sallah da masu sujjada da wuta ba a ranar da mutane zasu tsaya gaban ubangijin talikai.
#FreeZakzaky

Sheikh Adamu Tsoho Jos kwanakin baya a ziyarar da ya kai garin Potiskum cikin dakin Littattafan da Hujjatul Islam Malam Maina |

Tags:
Munasabobi