ABIN DA YA FARU A JOS.


Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates. Tare da -Idishia Jos.
                                                                           
A safiyan jiya aka wayi gari da jita-jitan rikici a garin Jos, wanda kuma daga bisani abin ya zama tashin hankali matuka, wannan abin dai ya faru ne a tsakanin hanyar Ring-Road da Unguwan Dutse Uku da Unguwan Mai-Damusa. Mun tattauna da wani bawan Allah Wanda yace a boye sunan sa kuma yana daga cikin Hukuman sakai na masu aikin bada gudumawan  gaggawa, mun tambayeshi dangane da wannan iftila'i da ya auku kuma ya shaida mana tare da karin bayami yake cewa; Lallai an wayi gari ne da jita-jita cewa gari ba lafiya musamman yankin Unguwan Dutse Uku nan.

Daga baya kuma sai aka ga wuta na tashi a wani gida an cinna mata wuta, su kuma al'umma sai labari ya fantsama cikin su ba abinda yake faruwa rikici ya barke tsakanin Hausawa da Kiristoci. Nan take akai ta kai komo ana rushe-rushe da jiwa juna jiwo, sai kuma jami'an tsaro suka zo wajen amma duk da zuwan jami'an tsaron bai hana rikicin cigaba ba Unguwan Mai-Damusa kuma itama ta dauka da karar harbe-harbe tare da rusa gidajen juna.

Mun kara tambayanshi ko zai shaida mana gidajen da aka rusa sun kai nawa? Yace mana lallai gidaje sun kai Goma a jimilla kamar yadda ya turo min ta kafar sada zumunta na WhatsApp. Ya kara da cewa a yanzu haka akwai wanda aka jiwa rauni da dama kuma suna asibiti daban-daban dake kusa da wajen da rigimar ya faru wasu kuma ana gida ana musu jinya. Daga faruwan abin sun kai taimakon su inda aka ajiye majinyatan asibiti da dama sun bada nasu gudumawa ga wanda aka jiwa rauni.
Mun tambayeshi  ya batun asarar rayuka kuma ?

Ya shaida mana anyi asarar rayuka amma a yanzu basu tantance ko guda nawa ne suka mutu ba gaskiya don banda adadin yanzu haka a hannuna kuma a tsarin aiki namu bama fadan adadin rayukan da suka mutu ma sai an gama kididdigewa amma sai tabbas anyi asarar rayuka. Mun nemi ya shaida mana ta fannin asarar Dukiya yakuma ce! Anyi asarar dukiya don ayi kone-kone an rusa gidaje da dama kaga kuwa dole ayi asarar dukiya ba kadan ba.

Muna so muji menene ya hada wannan rigima da yaki ci yaki cinyewa?

A to a gaskiya ba zan ce ga abinda ya hada ba amma dai labarin da yafi shahara shine  a kwanaki baya akace an kashe wani yaro daga bangaren Kiristoci to shikke nan dai aka wayi gari da jin jita-jita har abin ya zama tabbas. Mu dai a kunkiyance mun yi iyakan kokarin mu wajen tallafawa tare da wasu Doctoci anan wajen. Amma yau Litinin Alhamdulillah abin bai cigaba Ba an samu Zaman lafiya

Karshen abinda muka iya hada muku kenan a cikin wannan roho na abinda ya faru jiya a garin Jos na tashin hankali da aka samu. Ku kasance tare da Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates a koda yaushe don samu labarai masu inganci da sahihan abubuwan da suke faruwa tare da labaran duniya na yau da kullum.

#FreeZakZaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post