_ABIN DA YA BIYO BAYAN YUNKURIN KASHE SHEIKH ZAKZAKY A SHEKARAR 2009_

Ci Gaban rubutun mu na jiya.

_Bayan wannan bayani na Shaikh Zakzaky da mako guda, a ranar Juma’a 18/9/2009, aka gabatar da Muzharar Qudus ta shekarar 2009, wacce aka saba gabatar da ita a duk Juma’ar qarshen watan Ramadan. An gudanar da Muzaharar lafiya, sai da aka zo gab da rufewa, jami’an tsaron ‘yan sanda, qarqashin wani kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna a lokacin, mai suna Tambari Muhammed Yabo, suka zo suka bude wuta a kan masu Muzaharar a daidai Qofar Doka, Zariya, inda suka kashe mutum biyu; Shahid Musa Muhammad Jaji, da Shahid Abdurrahman Soje. Tare kuma da jikkata wasu da dama. Duk wai a qoqarinsu na huce fushin yunqurin kai hari gidan Shaikh Zakzaky da Allah ya hana su ikon aiwatarwa.

Nufin kashe Shaikh Zakzaky da Umaru Musa ‘Yar’adua ya yi, ya kwaranye ne sakamakon bayan wannan yunqurin ba jimawa Allah ya tsananta rashin lafiyar shugaban qasa Yar’adua, inda ya tafi jinya qasar Saudiyya a ranar 23/11/2009. A ranar 5 ga watan Mayun 2010 aka bayyana mutuwarsa, inda ranar 6/5/2010 ya bayyana a akwatin gawa bayan ya kwashe fiye da watanni shida yana fama da ciwon zuciyar da ita ta yi sanadiyyar mutuwarsa.Da yake yunqurin kashe Shaikh Zakzaky wata kwangila ce daga Amurka da Isra’ila kamar yadda Shaikh Zakzaky din ya fadi a jawabin da ya gabata, sai ya zama wanda ya maye gurbinsa, wato Goodluck Ebele Jonathan, ya dora da yunqurin yin kisan ba dare ba rana.
_____________________________
Ma'asuma Nigerian News Update.
[MUNCIRO DAGA LITTAFIN YUNKURIN KASHE SHEIKH ZAKZAKY A SHEKARU GOMA]
Wakilinmu;
   ®__Mahadi Tukur Almizan.

Follow Us on;
    Facebook
Ma'asumiyya Nigeria News Update.
          Blogspot
Www.maasumablogspot.com
            Youtube
MA'ASUMAH NIGERIA NEWS TV.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post