A KADUNA MA 'YAN SHI'A SUNYI TURURUWA AKAN TITUNA DOMIN NEMAN A SAKAR MUSU SHUGABAN SU


Daga wakilanmu Ammar Ummar Udawa da
Fatima Xahra Shi'ee

*Ma'asumah Nigeria News Updates*

A cigaba da gudanar da Zanga Zangar Lumana da mabiya Mazhabar shi'a kuma Almajiran Mlm Ibraheem Zakzaky (h) Sukeyi domin Neman ganin an Saki Shehin Malamin (H) da matar shi domin yaje yaga kwararrun likitoci don duba lafiyarsa, kamar yadda likitoci suka bayyana, Yau 'yan Uwa na garin Kaduna suka gabatar a yammacin yau ranar laraba 29/05/2019 na zariya kuma acikin daren nan tare da sauran sassan kasarnan kamar abuja dss.



ZANGA-ZANGAR Wanda akai mata (Suna,) KUBAR ZAKZAKY YAJE YAGA KWARARRUN LIKITICI, Wanda ta faro daga Kabala kwastin, kan babban titin dake zuwa Zariya daga Kaduna.

Shaikh Aliyu Turmidhi ya jagoranta, kuma shiya gabatar da jawabin rufewa, dajan kunnen Azzalumai wajen gaggauta sakin jagoran Harkar Musulunci Sheikh Ibrahim Zakzaky(H), an dai kammala lafiya.

—29/05/2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post