Happy Birthday Imam Hassan Almujatapha (as) |
Wata rana an taba ce masa: “Me ya sa ba mu taba ganin ka ki amsawa mabukacin da ya tambaye ka ba?” sai ya amsa da cewa:
“Hakika ni ma mai rokon Allah ne, kuma mai kwadayi gare Shi; don haka ina kunyar in zama mai roko alhali kuma ina hana mai roko. Kuma Shi (Allah) Ya sabar da ni da bayar da ni’imarSa gare ni, haka ni ma na sabar da Shi in bayar da ni’marSa (da Ya ba ni) ga mutane; to ina tsoron in na yanke al’adata Shi ma Ya yanke al’adarSa”.
Haka nan Imam Hasan (a.s.) ya taba sayen wani lambu daga wasu mutane Ansarawa da kudi dirhami dari hudu, sai labari ya zo masa cewa (wadanda suka sayar masa din) sun koma suna bukata daga mutane, sai ya koma musu da lambun ba tare da ya karbi kudinsa ba.