'YA'YAN MU SUNE JARIN MU, SAUKAN KARATUN ALKUR'ANI MAI GIRMA A GARIN ZARIYA.

A yau aka yi bikin yaye Dalibai Mahaddata Alkur'ani Mai Girma a Fudiyyah dake Garin Zariya. Bikin dai an fara tun da safe inda aka gudanar da abubuwa da daman gaske, mutane da daman gaske ne  suka samu halarta. An samu manyan baki daga waje daban-daban na cikin garin Zariya dama wajen Garin Zariya.



Sheikh Adamu Tsoho Jos yana mika Kyaututtuka a Dalibai Mahaddata Alkur'ani wanda aka yaye su yau a Fudiyya Zariya


Sheikh Adamu Tsoho Jos yana daga cikin manyan Baki da suka samu halarta Kuma yayi jawabi akan darajan Ilimi da muhimmancinsa. Sheikh Abdulhamid Bello shima yana daga cikin manyan baki da suka samu halarta. A karshe an mika kyaututuka na musamman ga wasu daga cikin Dalibai a yayi taron sannan anyi hotunan tarihi.

Ga wasu daga cikin hotunan da Malam Aljasawi ya dauko muku.

   --Idishia Jos.

#FreeZakzaky



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post