YAU LIKITOCI SUN GA SHAIKH ZAKZAKY .

Likitoci Daga Kasar Waje Sun Fara Duba Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah a yau Alhamis 25/4/2019.
Wannan hoton Shaikh din ne tare da Likitocin nasa a yau Alhamis.

Shaikh Ibraheem Zakzaky na tsare tun fiye da Shekaru 3 da suka gabata, duk kuwa da yau fiye da Shekaru biyu da kotun Nijeriya a Abuja tace a sake shi a biya shi diyyar tsarewar da aka masa ba bisa ka'ida ba.
A ranar 22 ga Junairun 2019 ne babban lauyan Shaikh Ibraheem Zakzaky, Mr Femi Falana SAN, ya mika bukata ga kotu a kan ta bari a bar Shaikh Ibraheem Zakzaky ya je ya nemi magani a wajen kwararrun Likitoci a waje. 

Sai kotun ta ba da umurni a zo da Likitocin daga ko ina su duba Shaikh din su ga yanayin jikinsa sai su ba kotu rahoto, sannan ta duba yiwuwar bari a fita da shi ko ai masa magani a nan.
Shaikh Zakzaky na fama da rashin lafiya sosai, sakamakon harbin da sojoji suka masa a kafa da hannu da ido, har ya zama ya rasa idonsa guda daya.

Haka ma Matarsa Malama Zeenah Ibraheem, ta na fama da raunin harsasai a yayin da har yanzu akwai wadanda ba a cire su a jikinta ba, har ma ba ta cika iya tafiya da kafarta ba.

Sai dai ba a saka ranar da za a koma kotu don cigaba da haramtacciyar shari'ar da gwamnatin Kaduna ta shigar da Shaikh Ibraheem Zakzaky ba, wanda yake saura kwanaki 8 a cika shekara guda da fara zuwa kotun da Shaikh Zakzaky, amma ko fara shari'ar ba a yi ba.

Muna fatan Allah Ya baiwa Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya lafiya, ya gaggauta fitowar sa da hallaka duk mai hannu wajen cuta masa.

Allah ka gaggauta fito mana da jagoranmu.

#FreeZakzaky

Daga -Idishia JOS wakilin Ma'asumah Nigerian News Updates

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post