Mas'udu dan masani tare da musa hassan shinkafi lokacin da suka tsaya garin kaura akan hanyarsu ta dawowa daga mu'utamar wakilan ma'asumah a garin katsina |
* MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES *
Tabbas, mafi yawa daga cikin Sahabban Ma'aiki (S.A.W.W) sunyi ridda (immediately) bayan wafatinsa (S.A.W.W). Sai dai ita wannan riddar ba ana nufin barin muslimci bane, a'a, suna nan cikin muslimcin nasu, sai dai sun juya baya ne daga wasicin Annabi (S.A.W W).
Irin wannan ridda ba ta fitar mutum daga muslumci, amma tana iya tabbatar da mutum a wuta kamar yadda wasu masu sallah za su dawwama cikinta sakamakon munanan ayyukansu.
Bari mu leqa cikin Bukhari mu ga abinda ya kawo game da wannan maganar tawa.
Ya kawo cewa,
Ibn Ibrahim Munziril-Hizamiyyu ya bani labari, Muhammad Bn Fulaihi ya bani labari, babana ya bani labari yace, Hilalu Bn Aliyu ya bani labari daga Ada'i Bn Yasari, daga Abu Huraira, daga Annabi (S.A.W.W) yace,
Ibn Ibrahim Munziril-Hizamiyyu ya bani labari, Muhammad Bn Fulaihi ya bani labari, babana ya bani labari yace, Hilalu Bn Aliyu ya bani labari daga Ada'i Bn Yasari, daga Abu Huraira, daga Annabi (S.A.W.W) yace,
" INA NAN A TSAYE SAI GA WASU JAMA'A, HAR SAI NA GANE SU (wane ne da wane da wane) SAI WANI MUTUM YA FITO TSAKANINA DA SU YACE, " Ku zo nan "! SAI NACE, INA (za ka tafi dasu) ? SAI YACE, " Wallahi zuwa wuta"! NACE, MENENE SHA'ANINSU ? YACE, " Lalle su sunyi ridda a bayanka ne kusa-kusa"! SANNAN SAI GA WASU JAMA'A, HAR SAI NA GANE SU SAI WANI MUTUM YA FITO TSAKANINA DA SU YACE, " Ku zo nan "! NACE, INA ? YACE, " Zuwa wuta wallahi "! NACE, MENENE LABARINSU ? YACE, " Ai sunyi ridda ne a bayanka kusa-kusa"! BA ZAN BAR GANINSA BA YANA KEBEWA DA WASU (Zuwa wuta) SAI 'YAN TSIRARU (daga cikinsu) ".
(Bukhari, Hadisi mai lamba 6587).
Saboda haka maganar riddar Sahabbai ba qarya bane, kuma za su tafi wuta kamar yadda Annabi (S.A.W.W) ya tabbatar.
Daga wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034