Daga Shafin Ma'asumah Nigeria News Updates
Tare da wakilinsu --Idishia Jos
Miliyoyin Al'umma ne suka saurari jawabi rufe Muzaharar, da farko Sheikh Muhammad Abbare ya gabatar da Malam Auwal Muhammad Gangare Jos wanda ya karanta paper na (Article) a wajen rufe muzaharar, kuma ya karanta ne da harshen Turanci kamar yadda aka rubuta. Bayan ya kammala gabatar da paper da Harisawa suka Fitar an Gabatar da Professor Abdullahi Yahya daga A.B.U Zariya Inda ya cigaba da jawabi a wajen.
Professor yayi kirane akan lallai Gwamnatin Buhari ta gaggauta sakin Malam ba tare da wata ka'idaba. Yace a yau Sayyid Zakzaky ya cika shekaru 68 a duniya shiyasa muka fito wannan zagaye domin taya shi murna. Malam Zakzaky rayuwansa Rayuwane na hadin kan mutane rayuwan ne na zaman lafiya wanda ya koyawa dukkan almajiransa. Kuma ba zamu bar Abuja ba har sai an sako mana jagoranmu Sayyid Zakzaky (H).
Professor ya kara da cewa, Duk da mun sani Malam yana gama da rashin lafiya tare da matar sa kuma ga ciwon idon yana damunsa amma Gwamnatin Buhari taki sakin sa domin yaga likita, kuma insha Allah ko basa so Malam zai dawo cikin nan bada jimawaba.
Daga bisani kuma An bada abin magana a Dr Sunusi Abdulkadir domin ya yi nasa jawabin. Dr Sunusi Abdulkadir yace; Muna mika alhinin mu ga Sayyid Zakzaky wanda aka kashe'Ya'Yansa wanda aka rusa masa gida aka harbeshi aka harbi matarsa, muna taya Jagoranmu Sayyid Zakzaky murnan wannan rana. A lokaci guda kuma muna taya Sahibul Asari Wazzaman murnan wannan rana wanda kuma shine zai kawo adalci akan zalunci.
Dr Sunusi Abdulkadir Kano ya kara da cewa; Idan muka shirya Allah zai iya bayyana Imam Mahdi (Aj) a kowanne lokaci kuma yace idan Sahibul Asar Wazzan ya bayyana Allah kasa mu daga cikin mataimakansa na hakika. Daga karshe yayi kira ga 'Yan uwa dasu taimakawa Jagora ta kowanne hali domin fitowan mu shine zai sa wannan Gwamnati ta saki Sayyid (H).
Daga karshe Hujjatul Islam Sheikh Adamu Tsoho Jos shin ya rufe muzaharar Da addu'a india aka kammala lafiya kuma an tashi Lafiya.
#FreeZakzaky.

Tags:
Labaran Duniya