MU'UTAMAR! MU'UTAMAR!!

Mu'utamar Na Dandalin Matasan Harka Islamiyya na Yankin Daura, Karo na 4.

Mu'utamar na Matasan Harka Islamiyya Karkashin Jagorancin Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) na Yankin Daura da kewaye na cigaba da gudana yanzu haka, Anje hutun Sallah da cin abinci.

Mu'utamar din wanda aka shirya na yini daya da farko Bayan Register na Mahalarta taron da kuma bude taro da Addu'a, Da Farko an Saurari Jawabi a kan Muhimmancin Ilimi daga Malam Aminu Abubakar Kofar Arewa inda Malamin ya tabo bangarori da dama a kan ilimi da kuma 'Kalu Bale' dake fuskantar Matasa a wannan lokacin.

Mai Jawabi na biyu Shine Wakilin Yan Uwa na Da'irar Karkarku Malam Sadiq Muhammad Karkarku inda yayi Magana akan 'Yunkurin Kafircin Duniya akan Harka Islamiyya'.

Daga karshe an gabatar da Maudu'in 'Muryar Matasa' inda aka saurari ra'ayoyin Matasa da kuma tsokaci daga Malam Shamsu Mashi, aka yi addu'a.

Mu'utamar din zai cigaba da gudana Bayan an gabatar da Sallah da Cin Abinci.

Ga Wasu daga Cikin Hotunan taron.








®ISHAQ SAGIR MAGAJI
#FreeZakzaky
20/4/2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post