Yau kimaninin sati (3), Ladan Muktar Ladanin Babban Masallacin Juma'a na garin Katsina ya rasa Ladancinsa sanadiyyar ya bayar anyi Maludin Sayyeed Fatima da Imam Ali wanda aka gudanar 16/3/2019 da aka gabatar a garin Katsina Wanda almajiran Sayyid zakzaky suka Saba shiryawa duk shekara.
A bana an nemi ladan Malam Muktar Ladanin Babban Masallacin Juma'a na garin Katsina da Ya bude wasu kofofin masallacin juma'a don ya zamana yan'uwa sun hadu a Masallacin sabida nan ne za'a daga da muzaharar nanne aka shirya rufewa ayi jawabin karshe. Cikin ikon Allah hakan ya faru.
Daga baya sai muka samu labarin cewa dangin Muktar Ladan da wasu 'yan gidan Liman sun kai karar sa wajen Sarkin Katsina Ahj D.r Abdulmumini Kabir Usman cewa " Ladan Muktar ya zama dan Shi'a har ya fara bada Masallaci ana gudanar da Harkokin shi'a". Wannan dalilin ne yasa aka karbe makullan Maaallacin dasafkeshi daga Ladancin Masallacin.
Ko da yake Muntar ba shi ne nadadden ladan ba yana taimaka wa ne tun Mahaifinsu naraye Liman Lawai Allah yaji kansa da Rahama, abin yazo ga dan uwan sa Mlm Yahaya. Babu Wanda yayi ma Masallacin hidima ta tsawon Shekaru dayawa kamar Ladan Muktar.
Kafin binciken yadda abin ya faru a hakika Muna ma Ladan Mlm Muktar addu'a Allah sa Sayyida Fatima da Imam Ali su dafa masa. Masu kulle -kulle Allah Ya shirye su .don sayyida Fatima da Imam Ali dukkanmu Musulmi ne ba yan shi'a ba.