A dabi'ar dan'adam, yana son yabo cikin aikin da yake yi, wanda hakan ke taimaka masa wajen qara qaimi da dagewa kan wannan aiki nasa.
Musamman ma dan Nigeria, in dai za ka yabawa aikinsa to zai cigaba dayi, ko da kuwa ace ba lada za ka bashi ba. Wannan dalili yasa kake jin su a kafafan yada labarai suna yin batanci ga bayin Allah don cimma buqatun kansu. Wasu kuma ka gansu dumu-dumu cikin kokuwar ganin wani wanda suke so ya doru kan wata kujerar siyasa.
'Dan Nigeria yayi kama da dabba ta wani bangaren, domin za ka same shi yawanci ya fi nuna soyayyarsa ga wanda zai cutar da shi ko yake cutarsa, kuma ya dauki macecinsa a matsayin macuci.
'Dan Nigeria yana da qoqarin bada lokacinsa, dukiyarsa, tunaninsa da kuma iliminsa don bada kariya ga wanda yake so. Amma sakamakon kamantuwarsa da dabba sai aka sami qarancin tunani da rashin sanin ya kamata tare da shi.
Aikin bauta yake yi a fahintarsa, domin wai hakan biyayya ga shugaba ne. Allah ya hore masa qarfi har yana iya tura Motar zalunci da kafirci, amma a hakan ana kiransa malalaci.
Shi kuma a tunaninsa irin na dabbobi gani yake shi qarqarfa ne, sai ya cigaba da turawa yana Tusa yana zufa, yana cije baki da zazzare idanuwa, ana kiransa malalaci shi kuma yana cewa ai sai ka tabbatar cewa ni mai qarfi ne !
Annabi (S.A.W.W) na cewa,
" MAI QARFIN KAYAR DA MUTANE BA SHINE MAI QARFI BA, MAI QARFI SHINE WANDA YA MALLAKI ZUCIYARSA YAYIN FUSHI ".
Ni kuma nake cewa,
" MAI QARFIN TURA MOTAR KAFIRCI DA ZALUNCI BA SHINE MAI QARFI BA. MAI QARFI SHINE WANDA WANDA KE IYA TARE BULLET DA TANKA DON KAWAR DA ZALUNCI "!
Shima yasan hakanne shi yasa yake kiranku da malalata cima-zaune !
Daga wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034