____FILIN JAGORAN GASKIYA__
""KISHIN ADDINI NE MAFITA, BA NA QASA BA!""
__Inji Jagoran Gaskiya [Sayyid Zakzaky (h)].
_Na’am idan ma muna da al’umma, alal misali; kana iya cewa al’umma iri wadancan, kana nufin qabilu? Sai mu ce; idan wani ma zai iya qumajin qabila, ya yi fada don qabila, sai mu ce masa; mu muna da abin da yafi qabilanci, ya fi bangaranci da ‘yan qasanci! Wato muna da addini!Addinin nan namu kuwa, ya hana zama dan qasa, ya hana kishi ko qumaji na ‘yan qasanci, ya hana qabilanci, ya hana bangaranci.
Manzon Allah (S) yana cewa; “Wanda ya yi yaqi domin kare qabilarsa (don qabilanci), ba shi a cikinmu.” Wato ma’ana ba shi daga cikin jimlar Musulmi. Ba aikin Musulmi ne ya yi yaqi don kare qabila ba, yana yi ne don kare addini ne. Da aka tambaye shi; wani ya yi yaqi domin jarumtaka, wani ya yi yaqi domin ta’assubanci, wanne ne ya yi yaqi ‘Fisabilillah’? Sai ya ce; “Wanda ya yi yaqi domin kalmar Allah ta zama ita ce a sama, shi ne (ya yi yaqi) saboda Allah, shi ne ‘Fisabilillah’.” Ana yin yaqi ne saboda Alllah (‘Fisabilillah’). Saboda haka akan yi shahada ne ‘Fisabilillah’, amma ba a yi domin qabila, ba a yi domin qasa, ba a yi domin bangare.
Tana iya yiwuwa mutum ya ce min; ah, to yanzu abin da kake cewa a taqaice dai a koma ma addinin Musulunci ko? Sai na ce; eh haka ne. Abin da nake cewa kenan, ba ina wayo ba ne, haka ne ba wayo nake ba. Yadda Bature ma bai mana wayo ba, ya ce; Kafirci ya komar da mu, to Musulunci za mu koma!Dama shi ne Jininmu, shi ne gadonmu, shi ne alfaharinmu, shi ne tarihinmu, shi ne mu! To, ta yiwu wani ya ce; Ehen, za ka balle Arewa ne? Sai mu ce; a’a, mu dai Musulunci muka ce maka za mu yi, kuma Musulunci ba ruwan shi da Kudu ba ruwan shi da Arewa. Musulunci addini ne na Allah, kuma qasa ta Allah ce.
________________________
Ma'asuma Nigerian News Updates,
Jawabin Sayyid Zakzaky (h) daga Littafin ""Mulkin Mallakar Turawa""
Tareda wakilinmu,
©__Mahadi Tukur Almizan.