KALIFANCI AHLUL-BAITI KO SAHABBAI?
(KASHI NA BIYU)
DAGA TASKAR:
ADAMUN ADAMAWA
Ma'asumah Nigeria News Update.
Tare da Ni'imatullahi Muktar.
Tabbataccen abu ne a musulunci cewa Matan Annabi (S) basa cikin Ahlil-Bait da Allah ya tsarkake, ko wadanda ya wajabta yin biyayya, ko wadanda ake sanyawa a cikin salati, domin babu aya ko Hadisi Annabi (S) da ya fadi cewa Matansa Ahlul-Bait ne, hasali ma duk Hadisin Annabi (S) sun cire matansa ne daga cikin Ahlul-Baitinsa.
Misali, an ruwaito daga ummu-salma Matar Annabi (S) ta ce, "Ayar nan, Abin sani, Allah yana nufin tafiyar da kazanta daga gareku ahlal-bait, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa " (Suratul Ahzab, aya 33), ta sauka ne a dakina, sai Manzon Allah ya aika aka kira Aliyu da Fatima da Hassan da Hussain, sai yace "wadannan su ne iyalan Gidana" (duba Mustadrakus Sahihain, na Hakim 03-146). ummu-salma ta ce, "Ina kofar dakin, sai na ce, Ni ba na cikin Ahlul-Baitinka ne ya Manzo Allah?" sai Manzon Allah ya ce, " ke kina tare da alheri, (domin) kina cikin matan Annabi (S)" (Durrul-Manthur, 05 198. Tafsirin Ibnu Kathir, Juz'i na 03, shafi na 46, da sabani dan kadan).
A wata ruwaya Umma-Salma ta shiga dakin ne ta daga mayafin da Annabi (S) ya lullube Ahlul-Baitinsa da shi ne ta sanya kanta a ciki, sai Manzon Allah (S) ya janye mayafin daga kanta, sai ta ce masa, "Ni ba ni cikin iyalan gidan ka ne ya Manzon Allah? Sai ya ce Mata "ke dai kina cikin matan Annabi, kuma kina kan alheri".
Ita Ummul-Muminina A'ishah ta bada shaida kan su wanene Ahlul-Baiti, inda ta ce, "Manzon Allah (S) ya fito da safe tare da bargo baki, sai Hassan dan Ali ya zo ya shiga bargon, sai Hussain ya shiga tare da shi, sai Fatima to zo, (Manzon Allah) ya sanya ta a ciki, sai Ali ya zo (shi ma) ya shigar da shi ciki, sa'annan ya ce, daga gareku Ahlal-bait, kuma ya tsarkake ku tsarkakewa", (Sahihi Muslim, Kitabu Fadha'ilus Sahaba, Hadisi mai lamba 4,450).
Muhadu a ( kashi na 3).